150512 Kenia Terrorismus
May 17, 2012Ƙasar Kenya ta bi sahun ƙasashen duniya wajen yaƙi da ta'addanci a yankin gabashin Afirka, inda a shekara ta 2011 ta tura dakarun ta zuwa ƙasar Somaliya domin yaƙar mayaƙan ƙungiyar al-Shabab, waɗanda ta ɗorawa alhakin ƙaddamar da hare haren bama-bamai da kuma yin garkuwa da jama'a a 'yan shekarun baya bayannan.
Cikin shekaru da dama dai ƙasar Kenya ta kauce wa tsoma baki a rikicin Somaliya da ke makwabtaka da ita ta hanyar ɗaukar matakin soji. Sai dai tun a shekara ta 2006, ayyukan tarzoma da matsalar fari sun tilasta wa dubbanin 'yan Somaliya tserewa zuwa ƙasar ta Kenya inda a yanzu fiye da Somaliyawa 'yan gudun hijira dubu 500 ke zaune a sansanoni daban daban na ƙasar, gwamnatin Kenya ta ƙaddamar da yaƙi da ƙungiyar ne a watan Oktoban shekara ta 2011 sakamakon ɗora wa mayaƙan na al-Shabab ta Somaliya alhakin sace wasu 'yan ƙasashen ƙetare da ke ziyara a Kenyar. A bisa wannan dalililin ne, a cewar Emmanuel Kisiangani na cibiyar nazarin lamuran tsaro dake birnin Nairobin Kenya gwamnatin ta tura dakarunta:
"Yace Kenya ta dogara da wannan hujjar ce wajen tura dakarun ta zuwa Somaliya domin fatattakar mayaƙan al-Shabab, waɗanda ake ganin suna da hannu wajen ƙalubalen tsaron da Kenya ke fuskanta, tare da kawar da su daga iyakokin Kenya, in da hali ma da daƙile su baki ɗaya. Saboda haka, za ka iya cewar sun yi nasarar kawar da yiwuwar ƙaddamar da manyan hare haren ta'addanci a Kenya amma banda na ayyukan ta'addancin da ƙungiyar ke yi a yankunan."
Ƙarin dalilan Kenya na ɗaukar matakin soji a Somaliya
Kisiangani ya ƙara da cewar akwai kuma batun hare haren da aka ƙaddamar akan ofishin jakadancin Amirka dake Kenya da kuma wani hotel a birnin Mombasa waɗanda dukkanin su suka janyo mutuwar jama'a da dama, ga shi kuma a baya bayannan da wasu hare haren da suka shafi ƙasar ta Kenya kai tsaye da aka kai a biranen Nairobi da kuma Mombasa, wanda akan hakane rundunar 'yan Sandan Kenya ke buƙatar gurfanar da wani Bajamushe mai suna Khaled Ahmed Mueller da aka tsare a Pakistan cikin shekara ta 2009 domin amsa tambayoyi a Kenyar, kamar yadda kakakin 'yan Sandan Kenya Charles Owino ya yi ƙarin haske:
" Ya ce, muna nemansa ne saboda bayanan da muka samu da ke nuna cewar yana da alaka da ƙungiyar al-Shabab dake Somaliya wajen kai harin. Akan hakane muke son ya zo ya fayyace zarge zargen da ake yi masa."
Mafita ga rigingimun dake faruwa a yankin gabashin Afirka
Ƙwararru dai na da ra'ayin cewar mayaƙan ƙetare na tallafawa ƙungiyar al-Shabab cikin farmakin da take kaiwa a yankin gabashin Afirka, ko da shike kuma ba'a kai ga tantance irin hannun da suke da shi a hare haren da ake kai wa ƙasar Kenya ba. Amma a cewar Emmanuel Kisiagani na cibiyar nazarin lamuran tsaro a birnin Nairobin Kenya, abinda ya fito fili shi ne cewar al-Shabab na da masoya a Kenya, wataƙila har a cikin 'yan gudun hijirar Somaliya dake sansanonin Kenya. Masanin ya ce mafita ga matsalar ba ta tsaya ga matakin soji kawai ba:
" Ya ce tilas ne a shawo kan muhimman dalilan dake janyo ta'addanci kamar talauci da kuma rashin mahimman buƙatun rayuwa domin mutumin dake fama da talauci ko wanda aka hana ababen more rayuwa ne za'a iya yaudarar sa zuwa irin wannan tsattsauran ra'ayin."
Rashin gwamnatin tsakiya a Somaliya tun fiye da shekaru 20 kenan, ya taimaka gaya wajen taɓarɓarewar lamuran tsaro ba wai kawai a ƙasar ba, harma a yankin gabashin Afirka baki ɗaya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar