1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi da talauci a Kenya

Sadissou YahouzaMarch 31, 2009

Yaƙi da talauci tare da taimakon Ƙungiyar Welthungerhilfe ta Jamus

Yaƙi da talauci a duniya.Hoto: AP


A mafi yawan ƙasashe masu tasowa, ana fuskantar ƙarancin makarantu,asibitoci, hanyoyin zirga -zirga da sauran ababe na more rayuwa.A saboda haka da dama daga matasa majiya ƙarfi ke kwarara daga ƙawuka zuwa birane, da zumar samar abin sakawa baki salati.

saidai kamar yadda hausawa ke faɗi,wajen neman ruwa ne ake samo iska.Ma´ana maimakon cimma dadi, matasanna faɗawa cikin wani mummunan hali na ƙaƙa ni kayi a cikin unguwanin share wuri zauna dake kewaye da birane.

Wasu sun ma na tsintar kansu a cikin halayen shaye-shaye kokuma halin bera.

Don magance irin wannan matsalolin ne ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa, suka ɓullo da wani tsari, wanda a ƙarƙashinsa, suke tsara matasa kokuma mata,a cikin ƙungiyoyi domin neman na kai.

Ƙungiyar bada agajin abince ce ta Jamus mai suna Welthungerhilfe, ta tsara mata cikin ƙungiyoyi a kasar Kenya.

Ɗaya daga cikin wakilan matan wata mai suna Florence ta bayyana gamsuwa da wannan shiri, wanda a cewarta, ya taka mahimmiyar rawa, wajen tallafawa mazauna karkara:Muna gudanar da ayyukan a cikin ƙungiyoyi, kuma ta wannan hanya ce muke samun abinci mu da yaranmu.

A shekarun baya bayan nan, ƙasar Kenya kamar da dama daga ƙasashen Afirka ta yunƙura wajen yaƙi da talauci.To saidai duk da haka, har yanzu da sauran rina kaba, domin duk cikin mutum biyu ɗaya na fama da ƙazamin talauci.

Amma a cewar Axel Weiser, shugaban ƙungiyar Welthungerhilfe al´amura sun fara cenjawa a sakamakon tallafin da ƙungiyar ke baiwa manoma a karkara:

Akwai husa´o´i iri-iri na noma da muke koyar da su,muna la´akari da ƙasar noma, da kuma shukar da tafi dacewa.

Sannan wannan mataki na girka ƙungiyoyi, ya taimaka matuƙa ainun, wajen faɗakar da manoma.Ko da shike muna gudanar da wannan tsari cikin ɗan taƙaitacen lokaci, to amma yana matsayin zakaran gwajin dafi, wajen yaƙi da talauci cikin karkara, a dalili da nasarorin da ya cimma.

Matan da suka tsara kansu a cikin ƙungiyoyin, sun duƙufa wajen faɗakar da sauran mata, su bada haɗin kai ga wannan tsari, sannan sun tara ƙoƙunan bara ga wasu ƙarin ƙungiyoyin bada taimakon raya ƙasa.Malama Mary, ɗaya daga membonin ƙungiyar matan na Kenya, ta bayyana nasarorin da suka fara cimma:

Tun lokacin da muka fara haɗa kai domin yin aiki tare, muka fara samun nasarori.

A yanzu har mun samun kuɗin da suka bamu damar gina makaranta, kuma mun shiga tattanawa da wasu ƙungiyoyin bada agaji don su taimaka mana.

Ƙungiyar Welthungerhilfe ta Jamus,ta girka ire-iren wannan ƙungiyoyin yaƙi da talauci fiye da 400 a ƙasar Kenya.

Sannan ta tanadi wani mataki na haɗa ma´amila tsakaninsu ta yadda zasu ɗauki darussa ya junensu.

Babu shakka akwai ´yan matsaloli dake tattare da wannan tasri, to amma inji Axel Weiser, ba zasu yi ƙasa a gwiwa ba:

Duk abinda mutum ya fara jarabawa zai fuskanci matsaloli, to amma har kullum ana cikin koyo, saboda haka , a kwana a tashi, za a kaiwa wani lokaci, inda za a gudanar da ayyukan ba tare da matsalar komai ba.Cemma duk wanda yace za shi yaƘi da talauci ,ai ya san da kwanan cewar zai gamu da matsala, amma a shirye muke mu ƙalubalance ta.

Wasu daga mahimman matsalolin da ake cin karo da su , sun haɗa da rashin kyakkyawan hanyoyin zirga zirga, cikin yankunan karkara.

Ƙungiyoyn matan sun zargi gwamnati da kasa taɓuka komai, domin inganta harakokin zirga zirga.

Wannan matsala kuwa na hadasa babbar koma baya , wajen jigilar albarkatun noma daga karkara zura birane, inji shugaban ƙungiyar Welthungerhilfe:

Shigar da kaya daga karkara zuwa birni na buƙatar,hanyoyin suhuri.Wasu na amfani da jakuna.

Idan buƙatar shiga mota ta taso, baya ga rashin inganci hanyoyi, motocin sun jaggoggoɓe .

A cikin mota ɗaya,za a iya samun mutane fiye da 20 gauraye da kaji da dabbobi . Duk da haka, shiga motar sai wanda ke da kuɗi, abunda ke wuya a cikin karkara.

Saboda wannan matsala, manoma da dama basu samun ikon saida albarkatun nomansu, cikin kasuwannin birane.

Ta la´akari da tsananin rayuwa a yankunan karkara, ya zama wajibi ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa su ƙara himmantuwa wajen tallafawa mata da matasa ta yadda zasu daina kwarara cikin birane inji Hans Joachim Preuss Sakatare Janar na Welthungerhilfe, wanda ya cigaba da cewar: Mutane ba su tafiya daga karkara zuwa birane domin kallon silma, kokuma kwalta, abunda ya tura kusu wuta ne ya fita wuta zafi.

An yi watsi da harakokin noma a cikin karkara, wanda shine tushen arziki.

Muddun ana buƙatar dakatar da mutane cikin karkara, da kuma taƙaita ayyukan ashsha cikin birane, cilas sai an tanadi matakan inganta rayuwa a cikin karkara.

Gina hanyoyin zirga zirga, samar da wuraren ban ruwan garake, tsara manoma cikin ƙungiyoyi, inganta harakokin sadarwa, wasu kenan daga cikin mahimman ƙalubalen yaƙi da talauci a yankunan karkara.

Taimakon raya ƙasa dai batu ne da ya jima a cikin kanun labaran duniya.

Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da ƙasashe masu hannu da shuni sun sha ɗaukar burin bada tallafi ga ƙasashe masu tasowa , to saidai har yanzu al´umomin ƙasashen basu gani ba a ƙass.

Amma wani rahoto da hukumar taimakon raya ƙasa wato OECD, ta gabatar, ya gano cewar, a shekara da ta gabata ,an samu cigaba na kashi 10 cikin ɗari, idan aka kwatanta da tallafin da ƙasashe masu cigaban masana´antu suka baiwa takwarorinsu masu tasowa a shekara ta 2007.

Mawallafi: Mark, Kleber/ Yahouza Sadissou Madobi.

Edita:Umaru Aliyu