1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi ya ɓarke a kudancin Sudan

June 14, 2011

Dakarun gwamnatin Sudan sun kai sabin hare-hare ta sararin samaniya a yankin Kordofan na kudancin ƙasar

Hoto: picture-alliance/dpa

Majalisar Ɗinkin Dinkin Duniya ta sake kira ga gwamnatin ƙasar Sudan ta daina kai hare-hare a yankin kudu, wanda zai samu ´yancin kansa a wata mai kamawa.

Saidai duk da alƙawarin da ta yi na tsagaita wuta , gwamnatin Khartum ta kai hare-hare ta sararin samaniya a yankin Kordofan, inda a cewar wata ƙungiya mai zaman kanta wato Sudan Democraty First Group, mutane kusan 70 suka rasa rayuka.

A wani jawabi da ta yi jiya a birnin Addis Ababa na ƙasar Ehtiopiya, Sakatariyar harakokin wajen Amurika Hilary Clinton,ta yi kira ga Ƙungiyar tarayya Afirka, ta kara bada himma, wajen warware rikicin ƙasar Sudan:

"ƙasa ga wata guda ya rage kudancin Sudan ya zama wata sabuwar ƙasa a duniya.

Gwamnatocin yankunan arewa da na kudu, sun yi nisa wajen tabattar da ƙasashe biyu masu cikkaken yanci, to amma hare-haren baya-bayan nan, da dakarun gwamnatin Khartum suka kaddamar,babu shakka za su maida hannun agogo baya, saboda haka,yauni ya rataya gare mu mu dukufa domin samar da zaman lafiya."

A cewar rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya,kusan mutane dubu 100 suka tsere daga yankin Abyei bayan harin da sjojin gwamnatin Sudan suka kai.

 Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal