Yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Gaza
November 17, 2012Rundunar tsaron Isra'ila na cigaba da kai hare-hare ta sararin samaniya a zirin Gaza.
Daya daga wannan hari yayi kaca-kaca da cibiyar ƙungiyar Hamas da kuma ofsihin ministan cikin gida.
Ya zuwa wannan lokaci aƙalla mutane 40 sun rasa rayuka a Gaza, sannan uku sun kwanta dama a ɓangaren bamni Yahudu sanadiyar rokokin da Hamas ta cilla.
Bayan Firayim ministan Masar, shima ministan harkokin wajen Tunisiya, Rafik Abdel Salam ya kai ziyara zirin Gaza a wannan Asabar, inda ya taya gazawa alhini.
Gwamnatin Isra'ila ta umurci sojoji dubu 75 shiga cikin shirin takwana, a wani mataki na yunƙurin kai farmaki ta ƙasa a Gaza.
A wani jawabi da ya yi a birnin Alƙahira, Faramiyan Turkiyya Recep Tayib Erdogan, yayi tur da Allah wadai da matakin da Isra'ila ta ɗauka kan zirin Gaza.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu