1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙin basasa ya bazu a Siriya

June 13, 2012

Gwamnatin Bashar Al Assad na Siriya na aikata kisa tare da cin zarafin yara kanana a tashin hankali da ya gama ƙasar baki ɗaya

In this Wednesday, Feb. 22, 2012 citizen journalism image provided by the Local Coordination Committees in Syria and accessed on Thursday, Feb. 23, 2012, flames rise from a house from Syrian government shelling, at Baba Amr neighborhood in Homs province, Syria. A French photojournalist and a prominent American war correspondent working for a British newspaper were killed Wednesday as Syrian forces intensely shelled the opposition stronghold of Homs. (Foto:Local Coordination Committees in Syria/AP/dapd) THE ASSOCIATED PRESS IS UNABLE TO INDEPENDENTLY VERIFY THE AUTHENTICITY, CONTENT, LOCATION OR DATE OF THIS HANDOUT PHOTO
Hoto: dapd

A ko wacce shekara a cikin watan Yuni Majalisar Ɗinkin Duniya ke gabatar da rahoton ta na na shekara dangane da halin da yara ƙanana suke cikin a duniya na azabatar wa da feyɗe da kisa da sauran su da suke fuskanta.

Kwamishiniyar hukumar Radkhiya Coomaraswamy wacce ke wakiliyakwamitin na MDD da ke saka ido akan yara da suka tagayara a sakamakon yaƙi ta ce abinda ya faru a Siriya a cikin watannin baya baya nan na zaman babbar barazana ga yara kanana.Inda A karon farko a cikin tashin hankalin da ake yi,wani jami'in majalisar Herve Ladsous da ke lura da aikin kiaye tsaro ya baiyana cewa ƙasar ta shiga wani hali na yakin basasa.Sakamakon yadda gwamnatin ke yin amfani da manyan makamai atilare da tankokin yaƙi da kuma jiragen sama masu saukar ungulu na yaƙi harma da wasu jiragen da ke sarafa kan su akan yan adawar.kana kuma yara kanana waɗanda shekarun ba su kai ba suma suna cikin zaman fargaba dangane da yadda ake yi masu kisan kaji a akurki.

Fargaban Majalisar Ɗinkin Duniya akan makomar yara a Siriya

''Ta ce mun ga yadda ake dukan yara da wayar lantarki sannan a kashe gutun sigari a bisa jiginsu ta ce wannan irin azabtarwa wata hukuba ce dake da ban al ajabi'.Galibi dai waɗanan yara da ke ganin wannan azaba da arkane basu wucce shekaru tara da haifuwa ba, kuma sotari waɗannan yara ana soce su ne akan hanyar su ta zuwa makaranta a yi garkuwa da su saboda hakidar iyayensu ''ta ce tun da nake ban taɓa gani irin wannan kisan gila ba da ake aikatawa akan yara wanda ta ce ake buɗewa wuta sannan ta ce ga yara sojoji da gwamnatin Siriya ta ke sakawa cikin faɗan ta ce a ɓangaran yan tawayen dai ba mu shaida ba, ko da yake wasu sun ce a kwai yara soji.''

Hoto: AP

Tilas ne a dakatar da yuƙurin gwamnatin Assad na kisan jama'a a cewar ƙasashen duniya

Ƙasar Jamus ita ce ke jagorantar aikin kwamitin da ke yin nazari dangane da matsayin da yara suke cikin sa a cikin ƙasashe a lokaci yaƙi kuma Peter Wittig wakili ne na ƙasar a majaisar ''ya ce wannan al 'amari karara na nuna yada giya mulki ke dibars shugaba assad akan taasar da yake ci gaba da tafkawa, ya ce a kwai bukatar a dakatar da kisan jama'ar.A yanzu dai sa'a ta ƙarshe wacce ake sa ran samu ta kauda tashin hankakli na Siriya shi ne irin matsayin da ƙasashen China da Rasha zasu ɗauka waɗanda a can baya suka hau kujerar naƙi har so biyu wajan kada kuria'a a kwamitin sulhu na MDD.

Hoto: dapd

Daga ƙasa za a iya sauraron sautin wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala