Yaƙin neman zaɓen Siriya
May 15, 2014'Yan takarar zaɓen shugaban ƙasa a Siriya su uku, sun fara gudanar da yaƙin neman zaɓe. Shugaba Assad da ya yanke shawarar sake tsayawa takarar jagorancin ƙasar na tsawon wasu shekaru bakwai ɗin, na daga cikin 'yan takara ukun da ke shirin fafatawa a zaɓen irinsa na farko a ƙasar da ke ɗauke da 'yan takara da dama,wanda za a gudanar da shi a ranar 3 ga watan Yunin wannan shekarar. Abdallah Abdallah, shugaban yaƘin zaben ɗan takara, Mahir Hajjar, ya bayyana yadda yaƘin zaɓen ke gudana.
Salon gudanar da yakin neman zaben Assad
"Yau muka fara gudanar da yaƙin zaɓenmu. Za mu bi kan mutane,lungu-lungu don mu tallata ɗan takararmu. Su kuma yan ƙasa,daga ƙarshe, zaɓi ya rage garesu."
A ran 28 ga wannan watan ne dai, 'yan ƙasar ta Siriya da ke waje za su yi zabensu, sai dai wasu ƙasashen da ke nuna rashin halaccin shugabancin shugaba Bashar Assad, kamar ƙasar Faransa, sun ce, ba za a yarda a gudanar da zaɓen a ƙasashensu ba.
"Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Pinado Abdu Waba