Yaɗuwar wutar daji a Rasha
August 7, 2010Ƙasar Rasha na fiskantar masifar wutar daji mafi girma a tarihinta, inda a yanzu haka ya tilastawa mutane dayawa barin gidajensu a babban birnin ƙasar Moskow, inda mutane ke sa ƙelle don rufe hancinsu, yayin da yaƙin dake tirniƙe birnin ya ruɓɓan'ya har sau biyar. Yanzu haka dai wutar ta yaɗu zuwa tsakiyar ƙasar yau, yayin da iska mai ƙarfi ke ƙarawa wutar ƙarfi, inda yanzu haka a ƙalla mutane 52 suka mutu. An sauyawa jiragen sama dake sauka a birnin Moskow hanya, don rashin kyawun yanayi. Yanzu haka ana nuna damuwa kan tsaron ƙasar ta Rasha, yayinda wutar ta doshi rubbun makaman nukiliyar ƙasar. Mahukuntan ƙasar suna ƙara damuwa bisa yadda wutar ta nausa yankin yammacin ƙasar, ida aka taɓa fiskatar matsalar sindarin haɗa nukilya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas