Amurka: Ya alaka da Afirka in Trump ya ci zabe?
October 17, 2024Za a gudanar da zaben shugaban kasar ne a ranar bakwai ga watan Nuwamban da ke tafe, inda Donald Trump na jam'iyyar Republican zai fafata da mataimakiyar shugaban kasar Amurkan Kamala Harris daga jam'iyyar Democrats. Harris ta kasance 'yar takara ne bayan Shugaba Joe Biden ya hakura da neman tazarce, sakamakon sukar da ya sha kan koshin lafiyarsa. Abigail Gift daliba ce a Ghana, ta kuma shaidawa DW cewa ta so a ce Shugaba Biden ne zai zarce sakamakon zarge-zargen da Trump ya sha fuskanta ciki har da caccakar da ya yi wa wata 'yar jarida Elizabeth Jean Carroll.
#b#To amma Samuel Ofoso na da ra'ayin fatan ganin Trump ya lashe zaben saboda manufofinsa ga Afirka a lokacin da yake kan karagar mulki, inda ya ba da gudunmawa ta fannin bunkasa harkokin kiwon lafiya da raya kasa da kuma kyautata alaka mai kyau. A yayin da yake shugabancin Amurka, Trump ya yi kaurin suna wajen amfani da kalmomin cin fuska da nuna kyama ga wasu bangarorin Afirka. A duk lokacin da yake batun 'yan gudun hijira yayin da shi kuma Biden ya fi karkata kan harkokin kasashen ketare, kamar yadda Etse Sikanku malami a jami'ar nazarin harkokin aikin jarida ta Accra ya nunar. A shekara ta 2021 Joe Biden ya dare kan karagar shugabancin Amurka, kuma daga cikin manufofin da ya soke na Trump jim kadan da kama aiki shi ne dage haramcin shiga Amurka da Trump din ya kakaba a kan mutanen da suka fito daga kasashen Musulmi.