Al'ummar Gaza na mutuwa wajen karbar biredi da ruwa-Erdogan
July 22, 2025
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi magana da kakkausar murya a birnin Santanbul, inda ya ce al'ummar Gaza ba za su ci gaba da mutuwa a wajen rububin karbar abinci ba.
Karin bayani:Erdogan ya nemi a kakaba wa Isra'ila takunkumi kan makamai
Kalaman Erdogan na zuwa a daidai lokacin da shugabannin kasashe da gwamnnatoci ke ci gaba da kiraye-kirayen tsagaita bude a wuta a yankin Zirin Gaza, kusan a kowacce rana Isra'ila na kashe fararen hula musamman mata da kananan yara a wajen turmutsitsin karbar abinci.
Karin bayani:Turkiyya ta bukaci Amurka ta sa baki don tsagaita wuta a Gaza
Babbar Jami'ar Diflomasiyyar EU Kaja Kallas ta sake jaddada matsayar Tarayyar Turai na kawo karshen halaka fararen hula a Gaza. Ta kara da cewa ta tattauna da Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Gideon Saar kan bukatar dakatar da yakin da kuma shigar da kayan agajin jinkai Gaza.