1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChaina

'Ya kamata Amurka da Chaina su kasance abokan hulda'

April 26, 2024

Shugaban Chaina Xi Jinping ya fada wa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken cewa kamata yayi kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya su kasance abokan hulda ba hamayya ba.

Shugaban Chaina Xi Jinping ya fada wa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken cewa kamata yayi kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya su kasance abokan hulda ba hamayya ba.

 

Wannan dai shi ne karo na biyu da Blinken ya ziyarci Chaina cikin shekara guda, inda ya nuna ci gaba da aka samu tsakanin alakar kasashen biyu tare da neman Beijing ta dauki wani babban mataki ciki har da dakatar da tallafa wa Rasha.

Kamfanin ByteDance ya musanta aniyar sayar da TikTok

A yayin ganawar tasu a babban dakin taron nan na Great hall of the people na Beijing, Xi ya ce an samu ci-gaba a huldar kasashen biyu  tun bayan ganawarsa da Shugaba Biden  a watan Nuwambar 2023.

 

Xi ya kara da cewa yana sa ran Amurka za ta kalli ci-gaban da Chaina ke samu a matsayin wani abun a yaba, inda ya ce idan har hakan ta samu to za a kawo karshen matsalolin da ke tsakanin kasashen biyu.

 

Jamus ta cafke masu yi wa China leken asiri