Alamu na nuna cewar sojojin Koriya ta Arewa za su taimaki Rasha a yakin da take da Ukraine, lamarin da ya sa fadar mulki ta Kyiv ta yi magantu game da yiwuwar samun sabuwar abokiyar gaba.
Talla
Ta ya ya taimakon Koriya ta Arewa ga Rasha zai shafi makomar yakin da take da Ukraine, kuma mai Kasashen Yamma ke yi domin dakile wannan manufa? Hadin gwiwa a fannin tsaro tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa, ba wani sabon abu ba ne. Da ma dai a watan Yunin wannan shekara, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya je Pyongyang domin cimma matsaya kan kawancen tsaro da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un. Sannan a baya, an yi ta rade-radi game da matakin Koriya ta Arewa, na bai wa Rasha makaman atilari. Kuma tun a farkon shekara ta 2023 Hukumar Leken Asiri ta Ukraine ta bayar da rahoton cewar, wata bataliyar sojojin Koriya ta Arewa ta isa yankunan kasar da Rasha ta mamaye.
Wani sakamakon binciken da Hukumar Leken Asirin Koriya ta Kudu NIS ta fitar ya nuna cewar, Pyongyang na son samar da sojoji dubu 12 domin taimakon Rasha a Ukraine. Tuni ma dai, ta riga ta tura dakaru 1,500 zuwa birnin Vladivostok mai tashar jiragen ruwa na Rasha. A halin yanzu NIS na magana game da sojoji 3,000 da aka riga aka tura Rasha, wadanda aka tanadar wa shigar burtu na Rasha don boye sahu. Amma har yanzu Rasha ko Koriya ta Arewa, ba su tabbatar da faruwar lamarin a hukumance ba. Sai dai Nico Lange babban jami'in a Cibiyar Tsaro ta Munich (MSC), ya ce babu kamshin gaskiya a wannan zargi.
Shekara guda da fara yakin Rasha da Ukraine
A ranar 24 ga watan Fabarairun 2022, al'ummar Ukraine suka wayi gari da tashin bama-bamai daga kasar Rasha.
Hoto: Bulent Kilic/AFP
Bakar rana ga miliyoyin al'ummar Ukraine
A ranar 24 ga watan Fabarairun 2022, al'ummar Ukraine suka wayi gari da tashin bama-bamai. Sojojin Rasha sun mamaye kan iyakokinsu da Rashan da ma Belarus da kuma yankunan da Rashan ta mayar da su karkashin ikonta tun shekara ta 2014. An kai hari a Ukraine, tuni aka fara hadawa da hukumomin gwamnati da kuma ya fara shafar al'umma.
Hoto: Ukrainian President s Office/Zuma/imago images
Hare-haren rashin imani
Shugaba Vladmir Putin na Rasha, ya bayyana harin da "matakin soja na musamman". Yana son karbe iko da yankunan Donezk da Luhansk. Mazauna birnin Mariupol, sun kwashe mako guda a ginin karkashin kasa na gidajensu. Da dama sun mutu a karkashin gine-ginen da suka rushe, kamar wasu daruruwa da suka mutu a karkashin baraguzan ginin wani gidan kallo.
Hoto: Nikolai Trishin/TASS/dpa/picture alliance
Miliyoyi sun yi gudun hijira
Yakin na Ukraine ya janyo kwararar 'yan gudun hijira a kasashen Turai, wanda ba a taba gani ba tun yakin duniya na biyu. Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNCHR ta ce, zuwa watan Fabarairun 2023 'yan gudun hijirar Ukraine a Turai sun fi miliyan takwas. Poland ta karbi sama da miliyan daya da dubu 500. Miliyoyi daga yankin gabashi da kudanci, sun watsu a sassan kasar.
Hoto: Anatolii Stepanov/AFP
Karbe iko da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhia
A makon farko na mamayarta, Rasha ta karbe iko da yankuna da yawa a kudanci da gabashin Ukraine da ma wani bangare na arewaci musamman kusa da birnin Kyiv. Tun daga wannan lokaci, babbar tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhia da ke yankin kudanci ke karkashin ikon Rasha. Yakin ya shafi farfajiyar tashar. Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Kasa da Kasa IAEA ta ce a sanya shingen kariya.
Hoto: Str./AFP/Getty Images
Ba a san adadin wadanda suka rasa ransu a yakin ba
Babu wanda ya san adadin wadanda suka rasa rayukansu a yakin. Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kimanin fararen hula dubu bakwai da 200 da kuma sojoji dubu 12 sun halaka. Sai dai ta ce, adadin ka iya fin haka. Ba a san yawan sojojin Ukraine da suka halaka ba. A watan Disamabar bara, mai bai wa shugaban kasar shawara Mykhailo Podoljak ya ce sun kai dubu 13. Sai dai babu tabbaci kan adadin.
Hoto: Raphael Lafargue/abaca/picture alliance
Tashin bama-bamai a gadar Crimea
A farkon watan Oktbar 2022, an samu tashin bama-bamai a gadar yankin Crimea da Rasha ta mamaye. Bama-baman sun lalata wani bangare na gadar da fadar Kremlin ta gina, a kan titin Kerch. Rashan dai ta ce, wata mota ce makare da bama-bamai daga Ukraine ta tashi a gadar. Sai dai tuni mahukuntan Kyiv suka mjusanta wannan zargi.
Hoto: AFP/Getty Images
Munanan hare-hare a tashar samar da hasken wutar lantarki
Kwanaki kalilan bayan tashin bama-bamai a gadar Crimea, Rasha ta kai mummunan hari na farko a kan tashar samar da hasken wutar lantarki. Matsalar ta fi shafar biranen Lviv da Kharkiv. Tun daga lokacin, harin ya zama na yau da kullum. Saboda mummunar barnar da harin ya yi a tashar, kusan a baki daya Ukraine ana fama da rashin hasken wutar lantarki ko ruwa ko kuma abin dumama daki a kowacce rana.
Hoto: Genya Savilov/AFP/Getty Images
Yaki da kuma sajewa cikin kasashen Turai
Volodymyr Zelenskyi na aika sakon faifen bidiyo a kullum tare da bayyana halin da kasar ke ciki, kuma miliyoyin mutane na kalla. Shugaban ba wai daga al'ummar kasarsa Ukraine kadai ba, ya ma samu taimakon daukacin kasashen yammacin duniya. A karkashin jagorancinsa, sajewa da kasashen Turai ya kai wani matsayi. A yanzu, Ukraine na neman zama mamba a kungiyar Tarayyar Turai EU.
Hoto: Kenzo Tribouillard/AFP
Ukraine na fatan samun motocin yaki kirar Leopard-2
Yadda Ukraine za ta iya karawa da Rasha, ya dogara ne ga taimakon da za ta samu. Kasashen kawance karkashin jagorancin Amurka, na samar da miliyoyin dalar Amurkan ga fannin tallafin jin-kai da kudi da kuma sojoji. An tafka gagarumar muhawara kan aika manyan makamai, a tsakanin kasashen Yamma saboda tsoron matakin da Rasha za ta dauka. Amma Ukraine na son samun manyan tankokin yaki kirar Leopard-2.
Hoto: Ina Fassbender/AFP/Getty Images
Hotuna 91 | 9
Amma Ukraine na nuna damuwa game da karin goyon baya da Rasha ke samu daga kawayenta, saboda ana ganin shugaban kasar ta Ukraine Volodymyr Zelensky ya kasa samar da wani kwarin gwiwa daga Kasashen Yamma game da abin da ya kira "shirin nasara" a yakin Ukraine. Sannan kuma Ukraine na jin tsoron ka da Donald Trump ya lashe zaben shugaban Amurka a watan Nuwamban da ke tafe, saboda yana son katse taimakon makamai ga kasarsa. Trump dai, ya dora alhakin mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a Zelensky cikin wani faifan bidiyo. Sai dai matakin Ukraine na neman taimakon kasashen yammacin duniya kan sabon kawancen Putin ba zai iya samun amsa kafin zaben Amurka na watan Nuwamban ba, a cewar Nico Lange babban jami'in a Cibiyar Tsaro ta Munich (MSC).
Mai magana da yawun kungiyar tsaro ta NATO a Brussels na cewar, idan sojojin Koriya ta Arewa suka shiga fagen yaki a Ukraine hakan na alamta haramcin goyon bayan da Pyongyang ke wa yakin Rasha da kuma kara nuna irin asarar sojoji da Moscow ta yi a fagen daga. A daya hannun kuma, kasancewar har yanzu kungiyar Tarayyar Turai ba ta mayar da martani kan zargin tura dakarun Koriya ta Arewa zuwa Rasha ba. Amma Roderich Kiesewetter masani kan manufofin ketare na babbar jam'iyyar adawa ta CDU a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ya ce akwai bukatar kasashen Turai su hada gwiwa wajen mayar da martani mai karfi ga Rasha, inda ya ce dole ne Jamus ta sauya kamun ludayinta ta hanyar kara mika makamai ga Ukraine.