1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yadda jaridun Jamus ke kallon rawar Afirka a yakin Iran

Abdourahamane Hassane MAB
March 6, 2026

Afirka ta Kudu na cikin halin tsaka mai wuya sakamakon yakin da Iran ke gwabzawa da Isra'ila da Amurka, saboda kasar ta dade tana goyon bayan Iran, amma tana jin tsoron fushin Shugaba Donald Trump na Amurka.

Shugabannin Afirka na kaffa-kaffa kan yakin da Iran ke gwabzawa da Amurka da Isra'ila
Shugabannin Afirka na kaffa-kaffa kan yakin da Iran ke gwabzawa da Amurka da Isra'ilaHoto: Eduardo Soteras/AFP/Getty Images

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta wallafa sharhi game da tasirin yakin Iran na yankin Gabas ta Tsakiya kan kasashen Afirka. Ta ce yawancin kasashen Afirka na da kyakyawar hulda har ta cinikayya da kasahen, amma tun lokacin da aka fara yakin Iran, kasashe kalilan ne suka fito suka nuna takaicinsu saboda suna jin tsoron shugaban Amurka Donald Trump.

Wasu sun fito sun suna Amurka inda suka yi Allah wadai a kan hare-hare da ta kai, wasu kuma kasashen na yin suka a kaikaice ba tare da bayyana suna ba. Misali, shugaban Afirka ta Kudu wanda dama huldar kasarsa da Amurka ke tangal-tangal, na fatan samun ragewar kudaden harajin a kasuwanci tsakanin kasarsa da  Amurka.  

Shugaba Ramaphosa na Afirka ta Kudu na tsoron fushin Donald Trump kan yakin IranHoto: Jim Watson/AFP

Shugaban Afirka ta Kudun ya yi likimo ya saka wa bakinsa linzami a kan yakin Amurka Israila da Iran, musammun ganin yadda Iran da Afrika ta Kudu suke cikin kasashen BRICS amma shugaba Cyril Ramaphosa, ya gaza cewa komai, Sai dai ya bayyana wata sanarwa ba tare da ambato sunan Amurka ko Isra'ila ba. Jaridar ta ce baya ga shi, kasashen Afirka da dama da ke da hulda da Iran sun yi shuru saboda jin tsoron Trump

Nitsewar jirgun ruwa a Kasar Libiya

Sai jaridar Die Tageszeitung wacce ta wallafa sharhinta mai taken wani jirgin ruwan Rasha mai suna LNG ya nitse a gabar tekun Libiya bayan tarwatsewarsa. Jaridar ta ce da alama Ukraine ta kai hari kan wanan jirgin ruwan Rasha da jirgin sama marasa matuki. Amma bayan fashewa da gobara mai tsanani, jirgin ya nitse tsakanin Libiya da Malta.

Gabar ruwan Libiya na ci gaba da shiga kanun labarai tun bayan hambarar da GaddafiHoto: Yousef Murad/AP Photo/picture alliance/dpa

Jirgin yana dauke da iskar gas mai gurbata muhalli kuma ya tashi daga Murmansk a arewacin Rasha. Jirgin ruwan yana aikin safarar man fetur na Rasha da Iran da Venezuela, wanda  zuwa kashi 80% na fitar da man fetur na Rasha ana sarrafa su ta wannan hanyar. Daruruwan irin wadannan jiragen na cikin jerin takunkumin kasashen Yamma.

Kungiyar M23 na ta'asa a Kwango

A sharhin jaridar Zeit Online, ta yi tsokaci a game da mutuwar mutane 200 a rugujewar mahakar Coltan a gabashin Kwango wacce ta ce wani iftala'in ya sake faruwa a mahakar Rubaya a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. 'Yan tawayen M23 sun musanta alkaluman gwamnati kan adadin wadanda suka mutu. Ruguzawar ta faru ne a mahakar Rubaya, wadda kungiyar 'yan tawayen ta M23 ke iko da ita.

Kungiyar M23 ta fi kai hare-hare a wuraren da ake da arzikin ma'adinin coltanHoto: Camille Laffont/AFP

Kungiyar M23 ta musanta labarin gwamnatin Kwango game da lamarin  Fanny Kaj, wani mai magana da yawun 'yan tawaye ya ce mutane biyar ne kawai suka mutu. Sannan ya ce babu zaftarewar kasa.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ce kasar da ke kan gaba a duniya wajen samar da ma'adinin coltan wanda ake bukatarsa wajen kera wayoyin hannu na zamani da na'ura mai kwakwalwa da injunan jiragen sama. A cewar binciken wata hukuma ta Amurka (USGS), Kwango ta samar da kusan kashi 40% na ma'adinin coltan na duniya a shekarar ta 2023.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani