1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron 'yan jaridu na duniya

Ramatu Garba Baba
June 14, 2018

An kammala babban taron 'yan jaridu na duniya da tashar DW ke daukar nauyi a duk shekara, taken taron na bana shi ne "Rashin Dai-daito a Duniya" taron ya sami mahalarta kimanin 2000.

Global Media Forum GMF 2018

Batun wanzar da zaman lafiya a kasar Afghanistan abu ne da aka jima ana fatan gani a ciki da wajen kasar sai dai a yunkuri da aka yi a lokuta da dama ba a kai ga cimma nasara ba. Wannan na daya daga cikin batutuwan da taron na Global Media Forum ya yi muhawara a kai. taron ya kuma tattauan kan rashin samun dai-daito wajen bayar da rahotannin ta'addanci.