1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNa duniya

Yadda kamfanonin kera makamai ke arziki da yaki

Abdoulaye Mamane Amadou SB
March 26, 2026

Yayin da barnar da makamai masu linzami ke shiga kanun labarai da asarar rayuka a fagen daga, a gefe guda yake-yaken na azurta wasu a bayan fage. Yanzu ba tambayar ko yaki na samar da riba ba ne, wane ne ya fi amfana?

Cinikin makamai a duniya
Cinikin makamai a duniyaHoto: Rasid Necati Aslim/Anadolu/picture alliance

Ana auna tasirin yaki da adadin kwace yanki ko asarar rayuka da kuma cimma wata manufa ta siyasa, sai dai a zahiri akwai gagrumar ribar yaki da ba a faye tattaunawa ba a kai. Yaki sinadarin tattalin arziki ne mai karfi musamman ga masu kera makamai. Kamfanoni irin su Lockheed Martin da Raytheon Technologies da BAE Systems na murza kambunsu a yankunan da ake rigimar siyasa don samun riba.

Tasirin cinikin makamai

Cinikin makamai a duniyaHoto: Mustafa Ciftci/AA/picture alliance

Abin da ke bambanta masana'antar kera makaman tsaro ta zamani ba kawai tasiri ba ne, amma daidaito da girman riba wanda galibi ke karuwa a lokutan rikici ko yaki. "Tabbas an ga karuwar sayan makamai a kasashen musamman Najeriya, wacce ke wakiltar kaso 34 cikin 100 na makamai da ake saye a yammacin Afirka." inji Dr. Isa Abdullahi.

Yakin Ukraine da rikice-rikicen yankin Gabas ta Tsakiya da tashe-tashen hankulan sassan nahiyar Afirka, sun taimaka wajen ba wa kamfanonin kera makamai damar cin kazamar riba, to amma ta ya ya kamfanonin ke wannan ciniki? "Sau da yawa ana bayar da kudi a karbi makamai, wasu lokutan kuma, ana musanyar makaman da danyen mai."

Kasashen Amurka da China da Turkiyya Jamus da Burtaniya, sun fi mallakar kamfanonin kera makaman yaki. Bincike ya nuna yadda manyan kamfanonin jiragen tsaro sun samu ribar dala biliyan 922 a 2024 kadai. Wani rahoto da SIPRI ya fitar ya nuna cewa, kudaden shiga da kamfanonin kera makamai na duniya suka samu ya kai dala biliyan 632 a shekarar 2023 sakamakon mayar Rasha a Ukraine da rikicin Gabas ta Tsakiya. Yunkurin kare kai daga barazanar yaki na cikin abin da ke kara daga darajar kasuwannin makamai inji Majo Janar Yahaya Shinko mai ritaya, "Duk kasa mai tattalin arziki indai ba ta da tsarin tsaro, to tana fuskantar barazanar rashin cin gajiyar arzikinta."

Masu kera makaman

Cinikin makamai a duniyaHoto: picture alliance/dpa/dpa-Zentralbild

Babban kamfanin kwangilar makaman tsaro na Amurka Lockheed Martin da ke arewacin Bethesda a jihar Maryland, ya yi wa sauran kamfanonin kasar sama da 30 zarra, inda ya caba ribar dala biliyan 6 da 900 a 2023 da dala biliyan 75 a 2025.

Jamus ta fi kowace kasa a Turai samun kudin sayar da makamai, inda manyan kamfanonin kera tankokin yaki da rokoki Rheinmetall da Thyssenkrupp da Hensoldt da Diehl suka samu ribar dala biliyan 15 a shekara.

Manyan kamfanonin Turkiyya da China da Iran da Rasha da Isra'ila, sun samu falalar kasuwa mai karfi a wasu kasashen Afirka."Kungiyoyin masu tsatsauran akidu a kasashen Sahel na Afirka, sun kara wa kasuwar makamai tagommashi" a cewar Alkassoum Abdourahamane, masanin tsaro a yankin Sahel." Ya kara da cewa duk da haka, kamfanonin ba su auna ribar da suka saba samu ba a shekarun baya. "Sayen makamai ya ragu a Afirka da kashi 40 cikin 100 saboda wasu manyan masu sayen makamai kamar Maroko da Aljeriya sun cimma burinsu na tsaro." Alkassoum.

Yake-yake ba kawai suna haifar da riba ba ne ga kasashe ko kamfanoni, suna habaka bukatu a kowane mataki, misali dole a maye gurbin makamai masu linzami da alburusai da motocin sulke da jiragen sama na yaki da ake lalata su a fagen daga. Najeriya ce kan gaba a jerin kasashen yammacin Afirka masu sayo makamai daga waje "Muna sayen makamin drone a kan farashin Naira miliyan 150 kowane guda daya" Inji ministan tsaron Najeriya Christopher Musa.

Kusan kaso 40 cikin 100 na adadin makaman Najeriya daga kamfanonin ketare aka saya, kamar Super Tocano daga Amurka da JF-17 daga Pakistan, duk da yake tana sayen kananan makamai daga Italiya da Afirka ta Kudu da Faransa da wasu kasashen gabashin Turai.

Tasrin yaki a fagen kasuwancin

Cinikin makamai a duniyaHoto: RU-RTR Russian Television/AP/picture alliance

Yaki na tasirin a bangaren sauya kasuwannin hannayen jari na duniya. Hannayen jarin tsaro yawanci na tashi lokacin da rikice-rikicen suka ta'azzara, tare da nuna hasashen karuwar riba a bangaren tsaro. Rasha babbar wa kasashen duniya cewar kasuwar makamai ce a Afirka, "Daga 2018 zuwa 2023, Rasha ta sayar da kashi 22 cikin 100 na makamai a Afirka" inji Alkassoum. Kasashe irin Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar da Mali suna bukatar makamai daga waje "Afirka ta sayi makamai kashi 19 cikin 100 daga China" inji Alkassoum .

Kamfanonin tsaro na zamani ba su dogara ga sayar da makamai kawai ba, suna kara samun kazamar riba daga kwangilar kula da su da kuma horo na dogon lokaci. Sai dai wasu kasashe masu tasowa na karbar manyan makamai kamar yadda Dr. Isa Abdullahi masanin tattalin arziki a Najeriya ya shedawa DW "Gwamnatin Muhammadu Buhari ta sayi makaman da suka kai dala biliyan daya daga Amurka, amma ta biya wani kaso da danyen mai."

Cinikin makamai a duniyaHoto: Robert Ghement/EPA/dpa/picture alliance

Dangantakar da ke tsakanin yaki da masu kera makamai ba gamon katar ba ne, tsari ne. Kamfanonin tsaro sun shiga cikin tsarin tsaro na kasa, inda akasarin kasuwancinsu na zuwa ne kai tsaye daga kasafin kudaden gwamnati. Cibiyoyin cinikayya sun yi kiyasin cewar an samu hada-hadar makamai ta bayan fage ta akalla dala biliyan daya, wanda mafi akasri ke silalewa ga hannun kungiyoyin 'yan 'tadda.

Baya ga irin kazamar riba da yaki ke habaka tattalin arzikin kamfanonin kera makamai, amma radadin yakin ga dan Adam na nuna zahirin gaskiya kan halin da ake ciki na yadda watakila ake ta'azzara yakin da ake gani a wannan zamani don taimakawa manyan masana'antun kera makamai a duniya ta bayan fage.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani