1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaduwar COVID-19 a kasashen Afirka

March 17, 2020

Kasashen Afirka na daga cikin yankunan duniya da cutar COVID-19 ta yi jinkirin shiga cikinsu tare ma da sauki ta fuskar yaduwa, idan aka danganta da yadda take bazuwa a duniya.

Afrika Senegal Coronavirus Pasteur Institute in Dakar
Hoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Da fari dai kwararru sun yi mamakin yadda ta kasance kalilan na kasashe ne matsalar ta shiga a nahiyar, inda wasu ke cewa cutar na barna ne ba tare da an gano ba.

Sannu a hankali dai yanzu annobar ta shiga kasashe 30 a nahiyar, inda ake da akalla mutum 450 da ke dauke da ita.

To sai dai ta fi tsanani ne a arewacin Afirkar, cikin kasashen Masar da Aljeriya da kuma Morocco, yankin da mutum 10 suka mutu da ita.

A gabashin nahiyar mutum 20 ne ke fama da ita a cikin kasashen shida. 

Afirka ta Kudu mai karfin arziki, na da mutum 62 da suka kamu.