1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nau'in Delta na yaduwa a Najeriya

July 22, 2021

Nijeriya ta samu karuwar alkaluman wadanda suka kamu da corona a cikin mako guda a yayin da kasar ke fuskantar barazanar yaduwar sabon nau'in Delta.

Bildergalerie über die Varianten des neuen Coronavirus
Hoto: Christian Ohde/imago images

A wani abun da ke zaman alamu na barazana na zagaye na uku na annobar Covid19, Najeriya ta kalli karin da ya kai na kaso 77 cikin dari na yaduwa annobar a mako guda kacal. Duk da cewa, kasar ta share tsawon watanni kusan hudu tana ganin alamun sauki daga annobar,  a wannan watan Yulin da muke ciki, ya nuna alamun sake tashin annobar mai tasiri.
Wata kiddidigar hukumar kula da cututtuka a Najeriy (NCDC) ta ce a tsakanin ranakun 5-11 na watan Yulin, kasar ta kalli karuwar da ta kai kaso 77 cikin dari na yawan masu dauke da cutar. Jihar Legas da ke zaman tungar annobar, alal misali na kallon karuwar asara ta rayukan da ta kai ta mutane 456. Karin Bayani:  Fargabar corona nau'in Delta a Najeriya


Duk da cewa, a wasu jihohin an kai ga rufe cibiyoyin kwantar da masu dauke da cutar, jihar ta Legas da ke kallon bullar sabon nau'in na Delta, na da kusan mutane 2600 kwance a cibiyoyi dabam-dabam a cikin jihar. Sabon nau'in na Delta, kuma a fadar sabuwar kididdigar  hukumar NCDC ta fitar, ta saka ragowar samun waraka daga cutar da kusan kaso 87 cikin dari tsakani na masu dauke da cutar. Karin Bayani:  Najeriya: Matsalar kin zuwa gwajin corona
Har ya zuwa yanzu, kasa da kaso daya a cikin dari na al'ummar Najeriya miliyan 200 ne suka kai ga samun riga-kafin allurar da gwamnatin ta kaddamar. Fargaba da rashin imani dama kila karancin riga-kafin, ya saka al'ummar Najeriyar da daman gaske mantawa da batun riga-kafin kafin bullar sabon nau'in.

Akwai karancin allurar riga-kafin corona a NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images


To sai dai kuma kasar ta ce tana shirin komawa zagaye na biyu na riga-kafin bayan sa ran karbar karin allura miliyan takwas cikin watan gobe na Augusta. Ana kallon ta'azzarar sabon nau'in cutar ne a yayin da al'umma a sassan kasar dabam-dabam ke ci gaba da bukukuwan babbar Sallar da ke zaman al'ada. Karin Bayani:  Rashin Tsaro: Asarar rayuka a Najeriya
Duk da cewar dai an soke hawan sallah a jihohin kasar da daman gaske, ci gaban shagulgula da cudanyar al'adar, na iya kara jefa kasar cikin barazanar mai tasiri. Tuni Abujar ta ayyana wasu jihohi guda shida da ta ce na zaman na kan gaba a cikin barazana ta yaduwar annobar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani