1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yafe basussuka: Burkina Faso

November 29, 2005

Tun watanni 6 da suke wuce dai ke nan kasashe masu arzikin masana'antu na rukunin nan na G-8, suka yi ta shelanta yafe wa kasashe matalauta na duniya basussukansu. Ko wace fa'ida wannan matakin ke janyo wa kasashen nahiyar Afirka da ke cikin shirin ?

Ita dai kasar Burkina Faso, tana daya daga cikin kasashen mafi talauci a duniya. Amma a bangare daya kuma, tana daya daga cikin kasahen nahiyar Afirka, wadanda ake yabonsu a kasashen yamma da aiwatad da matakan rage yawan talauci da al’ummominsu ke huskanta. Tun cikin shekara ta 2000 ne ta fara aiwatad da wani tsarin da ta shirya tare da goyon bayan bankin duniya, na rage kaifin talauci da ke addabar al’umman kasar. Jami’an bankin duniyar dai sun yaba mata da abin da suke gani kamar irin nasarorin da ta cim ma tun da ta fara aiwatad da shirin. Kamar yadda wakiliyar bankin duniyar a kasar, Ellen Goldstein ta bayyanar:-

„Tun fiye da shekaru 10 ke nan da ake ta samun nasara a Burkina Faso. Kasar na samun bunkasar tattalin arziki na kashi 5 cikin dari a shekara a halin yanzu. A fannin tattalin raziki dai, kasar ta sami bunkasar noman auduga. Muna fata za ta ci gaba da wannan yunkuri da take yi na inganta bunkasar tattalin arzikinta. Ta hakan ne sauran yankunan da ba a noman audugar ma za su iya cin moriyar wannan fa’idar da ake samu.“

Kasar ta Burkina Faso dai, tana huskantar matsaloli da dama, wadanda suka hada da fari da karancin ruwan sama. Abin da ya sa kuwa ke nan, ba ta iya ciyad da duk jama’ar kasar, wadanda yawansu ya kai miliyan 12. An dai kiyasci cewa, fiye da rabin al’umman kasar, ba sa samun albashin da ya kai dola daya a ko wace rana. Ban da dai auduga, ana kuma noman dawa, da gero da shinkafa da masara da gyada a kasar. Kusan kashi 90 cikin dari na al’umman kasar ne ke sana’ar noma. Amma duk da haka, saboda matakan kariya da shingen da kasashe mawadata ke gindaya wa kayayyakin da ke fitowa daga nahiyar Afirka, kasar ta Burkina Faso ba ta iya sayad da kayayyakin nomanta a kasuwannin duniya kamar yadda ya kamata. Sabili da haka ne kuwa, a cikin shekaru 5 da suka wuce, kasar ta sami gibi na kimanin kashi 15 cikin dari a harkokin cinikayyarta da kasashen ketare. Duk da hakan dai, jamai’an bankin duniya kamar Ellen Goldstein na ganin cewa, matakan da gwamnatin kasar ke dauka na yakan talauci, matakai ne ingantattu.

Amma masu sukar lamiri na ganin cewa, har ila yau dai da saurar rina a kaba. kasar ba ta da kwararrun ma’aikata, kuma ba ta da kafofin horad da su, a lal misali a fannonin kimiyya da fasaha, da sufuri da dai sauransu. `Yan kasar kalilan da suka sami damar kwarewa a wasu sana’o’in kuma, duk wsun fice suna aiki a waje. A halin yanzu dai alkaluma sun ce kusan kwararrun ma’aikatan kasar miliyan biyu ne ke aiki a ketare. A nan kuwa kamata ya yi a dau sahihan matakai, wadanda suka zarce shirin da aka gabatar na yakan talauci, inji Abel Somé, wani masanin kasar a fannin tattalin arziki. Bisa cewarsa dai:-

„Shirin da gwamnatinmu ke bi wai don yakan talauci na da cikas. Ko kadan ba mu sami ragowar talauci ba. Kome na nan ne kamar yadda yake. A nawa ganin dai, kamata ya yi a sake alkibla, a bi wasu sabbin hanyoyi, idan da gaske ne ana son a cim ma wani sakamako. Kamata ya yi, alal misali a yi wa kafofin kasa garambawul, don a bai wa `yan kasuwa masu zaman kansu karfin gwiwa. Ta hakan ne za a iya samar wa mutane da dama ayyukan yi, da kkuma kafa sabbin sana’o’i ko masana’antu.“

To a nan dai tamabayar da za a iya yi ita ce, wace fa’ida wannan shirin na yafe wa kasashe matalauta basussukansu zai iya kawo wa kasa kamar Burkina Faso ? Bisa yadda aka tsara dai, duk abin da kasar za ta samu karkashin shirin bai wuce kashi 1 zuwa 2 cikin dari na kasafin kudinta ba. Hakan dai na nuna cewa ke nan, a cikin shekaru da dama masu zuwa nan gaba ma, ba za a sami wani muhimmin sauyi na rage gibin kasafin kudin da kasar ke ta fama da shi ba.

Yayin da kasashe mawadata ke ta kambama kansu da shirin yafe wa kasashe matalauta basussukansu da suka gabatar a Gleneagles dai, halin da ake ciki takamaimai a kasashe kamarsu Burkina Faso na nuna cewa, za a dade kasashe matalautan ba su fice daga dogaron da suke yi kan taimako da suke samu daga ketare ba.