Yajin ƙin cin abincin fursunonin Falasɗinu
February 24, 2013Domin nuna baƙin cikinsu ga mutuwar wani ɗan Falasɗinu da ke ɗaure a Israila, dubban fursunonin Falasɗinun da ke wurin sun shiga wani yajin ƙin cin abinci.
Kimanin Fursunoni dubu uku suka yanke shawarar ƙin cin abinci a wannan lahadin kamar yadda mai magana da yawun hukumar da ke kula da gidajen yari ya bayyana.
A bayanin da hukumomin Israila suka bayar, sun ce kwatsam sai wani magidanci mai shekaru 30 na haihuwa ya rasu ranar asabar, a ɗaya daga cikin gidajen kason da ke arewacin Israila, kuma suna kyautata zaton cewa bugun zuciya ce.
To sai dai a ɓangaren Falasɗinawan suna zargin cewa ya mutu ne sakamakon wahalan da ya sha wajen wani bincike.
Tuni dai Shugaban Falasɗinu Salam Fajjad ya buƙaci da a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar wannan mutumi.
Ƙungiyoyin magoya bayan wadanda ke ɗaure a hanun Israila sun ƙaru, suna kuma kira da a bi bayan Falasdinawa huɗun da suka shafe suna yajin ƙin cin abincin.
A wajen arangama da dakarun Israila a gaɓar tekun yamma da kogin Jordan masu zanga-zangar Falasdinu aƙalla 100 suka yi rauni
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita : Zainab Mohammed Abubakar