Yajin aiki a Portugal
November 24, 2010A ƙasar Portugal yajin aikin adawa da shirin tsuƙe bakin aljihun gwamnati na sa'o'i 24 da aka fara ya tsai da komai cik. Baki ɗayn ma'aikatan gwamnati da na masu zaman kansu suka shiga yajin aikin. Jiragen sama da na ƙasa da motocin kwasan shara da tashoshin jiragen ruwan duk sun rufe wuraren ayyukansu. a tsawon yinin yau. Wannan yajin aikin shi ne na farko tun shekaru da ya samu haɗin kan ma'aikata masu zaman kansu da na gwamnati. Gwamnatin ƙasar a shirinta na tsuƙe bakin aljihu, ta na son ƙara haraji kan kayan da ake sayarwa da kashi biyu cikin ɗari, kana za ta riƙe kuɗin fansho duk a ƙoƙarin da take yi na cika ƙa'idar ƙasashen Ƙungiyar Tarayar Turai da asusun ba da lamuni ta duniya wato IMF.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas