Yajin aiki ya gurgunta kamfanin Lufthansa na Jamus
September 8, 2015A wannan Talata yajin aiki matuka jiragen saman kamfanin Lufthansa na kasar Jamus ya gurgunta harkokin tafiye-tafiye. Tuni kungiyar matuka jiragen saman ta kai kamfanin kara saboda shirin daina daukan sabbin matuka jiragen sama karkashin dokokin gata na kwadago a Jamus.
Mai-magana da yawun kungiyar ya ce baya ga Talata da Laraba akwai yuwuwar kafin karshen mako a sake wani yajin aikin. Tuni kamfanin na Lufthansa ya soke tafiye-tafiye jiragen sama masu nisa 84 daga cikin 170, sannan akwai yiwuwar soke kashi biyu bisa uku na tafiye-tafiyen jiragen saman na ranar Laraba. Kamfanin
Lufthansa na Jamus ya kasance daya daga cikin jiga-jigan kamfanonin jiragen sama a duniya. Sai dai wannan yajin aiki bai shafi sauran da suke karkashin kamfanin Lufthansa kamar Germanwings da sauransu ba.