Yajin aiki ya janyo cikas a filin Jirgin saman Frankfurt
February 28, 2012Ma'aikata a babban filin jirgin saman birnin Frankfurt dake nan Jamus, waɗanda ke ci gaba da gudanar yajin aiki sun janyo - ala tilas- aka soke jigilar ɗaruruwan jirage a wannan Litinin, wanda kuma zai yaɗu ya zuwa Talatar nan musamman ga jiragen da za su yi jigilar cikin gida a Jamus da kuma a tsakanin ƙasashen tarayyar Turai. Ƙungiyar ma'aikata ta GdF tana shirya jerin yaje-yajen aikin ne bisa irin kuɗaɗen albashin da ake baiwa ma'aikata a filin jirgin, waɗanda ba na cikin jirgi ba, da kuma akan yawan sa'oin aikin su.
A baya bayannan ne kuma ƙungiyar ma'aikatan ta ce akwai muhimmancin gaske jami'an dake kula da sauka da tashin jiragen saman su bi sahun yajin aiki na tsawon sa'oi shidda a safiyar wannan Larabar domin nuna goyon baya ga 'yan uwansu. Matakin dai ka iya janyo mummunar matsala fiye da wadda ake fama da ita a yanzu. Kamfanin Fraport dake da alhakin tafiyar da harkokin filin jirgin saman na birnin Frankfurt ya ce salon yajin aikin na yanzu yana janyowa kamfanin asarar kuɗi kimanin Euro miliyan ɗaya a kowace rana.
A yanzun nan da ake batu dai hukumomin filin jirgin na yin amfani da ma'aikatan da ba su da wakilci a cikin ƙungiyoyin ƙwadago domin maye gurbin masu yajin aikin da nufin gudanar da jigilar kashi 80 cikin 100 na adadin jiragen saman da za su tashi, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙaucewa cuskoson matafiya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu