1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kanawa sun amsa kiran kungiyar kwadago

Nasir Salisu Zango RGB
July 26, 2022

Dubban mutane a jihar Kano ne suka amsa kiran kungiyar kwadagon Najeriya a gabatar da zanga-zangar kin jinin gwamnati na yin burus da yajin aikin malaman jami’a.

Nigeria | NLC Protest
Hoto: Nasir Salisu Zango

Jama'a da dama ne suka fito domin marawa Kungiyar Kwadago ta NLC baya a jahar Kano da ke arewacin Najeriya, wajen gabatar da zanga-zangar kin jinin gwamnati na yin burus da yajin aikin Kungiyar malaman jami’o'i wato ASUU da aka shafe watanni bakwai ana yi, zanga-zangar wacce ake gabatarwa a fadin Najeriya, 'yan kwadagon sun ce, dole su tursasa gwamnati wajen ganin ta kawo karshen wannan yajin aiki.

Boren ya hada kan dubban ma’aikata da dalibai ada suka fito cikin yanayin bacin rai domin gudanar da wannan zanga-zangar, dangane da yadda suke cewar gwamnatin tarayya ta kasa shawo kan yajin aikin malaman jami’o'i duk da cewar jami’oi'n kasar sun shafe watanni a rufe.

Kamred Kabiru Ado Minjibir shi ne shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya reshen jihar Kano, ya ce sun fito kwansu da kwarkwata domin goyon bayan yajin aikin kasancewar ya shafi kowa, sai dai ya ce bayan sun gama yajin aikin na wannan Talata, zuwa gobe Laraba za su tattara a babban birnin tarayya Abuja, bayan nan kuma za su bulowa gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayan gida domin kuwa bayan tiya akwai wata cacar. Ya kara da cewa, idan har yajin aikin bai sa gwamnati ta rusuna ba, to za su tafi yajin aikin gargadi, daga nan kuma su tafi yajin aikin sai baba ta gani.


Masu zanga zangar a Kano, sun tashi daga titin Mundubawa daga nan kuma suka yi tattaki zuwa fadar gwamnatin jihar har ma suka sami tarba daga gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa, har ma gwamnan ya bayyana farin cikin sa bisa yadda zanga- zangar ta zama ta lumana.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya yaba da zanga-zangar ta lumanaHoto: Nasir Salisu Zango

To ko wannan yajin aiki zai iya yin tasiri la’akari da yadda aka dauki lokaci ba tare da an shawo kan matsalar ba? Farfesa Sani Lawal Malumfashi masanin zamantakewar a Jami’ar Bayero da ke Kanon, ya ce tabbas yajin aikin zai yi tasiri.  Ya ce, ''yanzu haka ana kallon zanga-zangar a fadin duniya dan haka yana kara kunyata gwamnatin Najeriya a idon duniya bisa yadda take yi wa fannin ilimi rikon sakainar kashi a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tsaro''

Suma dalibai ba a barsu a baya ba wajen bayyana takaicin su dangane da yadda yajin aikin ya zame musu katankata na wai mutuwar bakin al'muru, nda suka bayyana yanayin kunci da ya jefa su. Daliban sun ce ya zama wajibi su goyi bayan duk wani yunkuri na tilasta wa gwamnati magance wannan yajin aikin, da yawan daliban na zargin cewar manyan kusoshin gwamnatin da za su magance matsalar yaransu ba a kasar suke karatu ba, shi ne dalilin rashin daukar matakin magance matsalar.

Yanzu haka ana kan jiran martanin gwamnatin tarayya akan wannan barazana ta Kungiyar NLC wacce ke cewar matukar gwamnati ba ta kawo karshen matsalar ba za ta tafi yajin aikin gargadi daga nan kuma ta kulle kasar gaba daya a yanayin yajin aikin sai baba ta gani.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani