Yajin aikin gama gari a Ethiopiya
March 5, 2018Talla
Daga cikin yankunan da yajin aikin ya fi samu karbuwa har da yankin 'yan kabilar Oromo kabila mafi rinjaye a kasar, kana masu adawa da gwamnatin. An dai kafa dokar ta bacin ne a cikin watan da ya gabata a jajibirin da firaminista Hailemariam Desalegn ya yi marabus.
Zanga-zangar nuna kyamar gwamnati, da 'yan kabilar na Oromo suka soma yi tun a shekara ta 2015 zuwa 2016 ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 940.