1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aiki a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB/MAB
February 27, 2023

Ana yajin aiki na kwanaki biyu da gamayyar kungiyoyin kwadago na Jamhuriyar Nijar suka kira kan rashin cika wasu bukatu da suka amince da gwamnati.

Jamhuriyar Nijar | Kungiyoyin kwadago
Kungiyoyin kwadagon Jamhuriyar NijarHoto: Salissou Boukari/DW

A Jamhuriyar Nijar a wannan Litinin gamayyar kungiyoyin kwadago 14 na UAS ne suka tsunduma cikin yajin aiki na kwanaki biyu, inda suke nema da gwamnati ta biya musu wasu bukatu da suka tambaya wanda suka ce tun shekara ta 2012 aka dauka musu alkawali amma babu cikawa. Hakan kuma ya biyo bayan wani yajin aikin na kwanaki biyu da kungiyar ITN da aiwatar a karshen watan Janairu da ya gabata.

Za a iya cewa yajin aikin na kwanaki biyu da gamayyar wadannan kungiyoyi suka kira ya samu karbuwa a wasu fannoni na ma'aikata da suke karkashin wadannan kungiyoyi, Sai dai kuma wasu bangarori da ke karkashin wannan kungiyar kwadago ta CDTN da ita ba ta kira yajin aikin ba na yin nasu aiki.

A fuskar ma'aikatar shari'a ma dai inda muka ziyarta kungiyar ma'aikatan ta SANAJ da ta kumshi ma'aikata da ke kama wa alkallai aiki sun bi wannan yajin aiki kuma ta bakin magatakardan wannan kungiya Maitre Souley Abdou Dodo, ya nuna gamsuwa da yadda magoya bayansu suka amsa wannan yajin aiki.

Daga daya bangaren jami'an kiwon lafiya na karkara kungiyar SYNASAT  sun bi wannan yajin aiki kaman yadda Abdoul Aziz Moussa ya tabbatar. Sai dai a nan birnin yamai idan aka yi la'akkari za a ga cewa a fannin zirga-zirgar ababen hawa kaman yan tasi da sauran masu sufuri na cikin gari da dama ba su amsa wannan yajin aikin ba kuma cewar Gamatie Mahamadou shugaban kungiyar UTTAN ya nunar.

Ya zuwa yanzu dai bamu ji labarin batun wata tattaunawa tsakanin gwamnati da su kungiyoyin da suka soma wannan yajin aiki na kyanaki biyu na yau Litinin da gobe Talata wanda ake ganin idan aka ci gaba da haka zai haddasa babban koma baya a fannoni da dama na rayuwa.