1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin ma'aikata a Kaduna saboda neman karin albashi

October 3, 2011

Ma'aikatan kiwon lafiya ta jahar Kaduna sun shiga yajin aiki, ya sanya tilas gwamnatin ta dauko sabbin daliban makarantun kiwon lafiya da unguwannin zoma wadanda basu kware ba don daukar nauyin kulawa da marasa lafiya.

Lafiya uwar jikiHoto: AP

Wannan yajin aiki ya shafi asibitoci ne da kuma marasa lafiya dake kwance a asibitoci daban daban mallakar jahar. To sai kungiyoyi da jami'an kiwon lafiya da masu kare hakkin bil
adama na ganin bai cancanta ba gwamnatin ta dauko dalibai, domin hallaka jama'a ne kawai zasu yi.
A yau dai an shiga kwana na 4 kenan da fara wani munmunar yajin aikin gama gari da ma'aikatan kiwon lafiya tare dana duba gari ta jahar Kaduna suka tsunduma saboda rashin cika masu alkawarinsu na karin albashi da gwamnatin ta dauki tsawon lokaci tana wasa da hankalinsu, lamarin dake yin nuni da cewa komai da komai ya tsaya chak a bangaren kiwon lafiyar talakawan kasa, alamarin da kuma harwa yau
ya jefa dumbum wadanda ke jiyya a asibitoci mallakar jahar kimanin 280 fadawa cikin fargaba da rashin isashhen kwanciyar
hankali.
Sakamakon sabon yunkurin da gwamnatin ta aiwatar nayo safarar daliban makarantun kiwon lafiya da na jami'o'I tare da unguwannin zoma dan taimakawa masu jinya.da kwararrun likitoci tare da nurse nurse da kuma masu ruwa da tsaki kan bunkasa bangaren kiwon lafiyar alumman ke nuna bacin ransu kamar dai yadda shugaban likitoci mata ta jahar Kaduna Miss Cicilia Musa ta bayyana.
Rahotanni sunyi nuni da cewa kwararrun masana a bangaren lafiya tare da kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bukaci ganin gwamnatin ta gaggauta sasantawa da kungiyoyin jami'an kiwon lafiya da kuma dakatar da aikace aikacen da dalibai masu koyan fida ke gudanarwa akan marasa lafiya.
Dr Ahmed Yande shine shugaban gamayyar kungiyoyin masu duba gari a jahar Kaduna. Ya bayyana yadda gwamnatin ke barnatar da miliyoyin kudaden talakawan kasa ga yan siyasa, maimaikon farfado da bangaren kiwon lafiyar al'umma dake cin karo da matsaloli.
Kwanaki 2 kenan dai da fara gudanar da aikace aikacen wadannan dalibai a cikin asibitocin wadanda suka hada da bada magunguna da yin allura da kuma sauran ayyuka da suka jibanci na kula da lafiyar alumma, da shugabanin kungiyoyin likitoci mata ke bukatar sarakuanan gargajiya da malaman addinai su matsawa gwamnatin wajan dakatar da munanan ayyukan da dalibain ke gudanarwa inji Miss Cicilia Musa.
Kokarin jin ta bakin gwamnatin dai yaci tura,to amma idan dai ba a manta ba an sha gudanar da tararrakin sasantawa dake ake watsewa baram baram ba tare da cimma waata matsaya daya ba,kuma mudden dai ba a cire wadannan dalibai da unguwannin zuma masu koyan aiki wadanda basu mallaki takardan kamala karatu ba, to fa rayukan talakawan kasa dake kyance asibiti na cikin hatsarin gaske.

Bukatar samun magunguna a asibitociHoto: Fotolia/Gina Sanders

Mawallafi: Ibrahim Yakubu

Edita: Umaru Aliyu