Yajin aikin malamai a Afirka Ta Kudu
April 24, 2013A wannan Larabar ce (24.04.2013) kungiyar malaman makaranta a kasar Afirka Ta Kudu ke yin yajin aikin gama-gari na yini daya game da gudanar da jerin gwano domin neman ministar kula da harkokin Ilimi a kasar ta yi murabus. Kungiyar, wadda ke zama reshe a cikin hadaddiyar kungiyar ma'aikata ta kasar, ta ce kimanin malamai 25,000 ne ke shiga a dama da su cikin jerin gwanon, da kuma yajin aikin.
Dama kuma kungiyar ma'aikata a kasar, ta nemi ministar Ilimin farko, Angie Motshekga tare da darekta janar a ma'aikatar kula da sha'anin Ilimin, Bobby Soobrayan su yi murabus, bisa tabarbarewar sha'anin Ilimi a kasar.
Sai dai kuma ma'aikatar kula da sha'anin Ilimi a kasar ta Afirka Ta Kudu ta yi barazanar ladabtar da duk wani malamin makaranta ko kuma shugaban makarantar Sakandaren daya kuskura ya shiga cikin yajin aikin.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman