1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakar cacar baka tsakanin Chadi da Sudan

April 17, 2006

A ci-gaba da yakin cacar baka tsakanin kasar Chadi da makwabciyar ta Sudan, shugaban Chadi Idriss Deby ya zargi gwamnatin birnin Khartoum da kokarin amfani da rikicin lardin Darfur don kawo rudami a ilahirin yankin tsakiyar Afirka. A halin da ake ciki gwamnatin shugaba Deby ta yi kira ga gamaiya kasa da kasa da ta tsoma baki a rikicin na lardin Darfur kana kuma ta kakabawa gwamnatin Sudan takunkumi. Wannan kiran ya zo ne kwanaki kalilan bayan wani harin ´yan tawaye akan babban birnin Chadi, N´djamena. Gwamnatin Chadi ta zargi Sudan da marawa ´yan tawayen baya, to amma Sudan ta musanta haka. Kwanaki 3 da suka wuce gwamnatin Chadi ta ce nan gaba ba zata iya ba da kariya ga ´yan gudun hijirar lardin Darfur su kimanin dubu 200 da ke cikin kasar ta ba.