1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yake-yake sun haifar da karuwar 'yan gudun hijira

Mouhamadou Awal Balarabe
June 20, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta fidda rahoto kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki a duniya inda ta bayyana cewar sun karu idan aka kwantanta da shekarar da ta gabata sakamakon yake-yaken da ake fama da su.

Niger Flüchtlinge aus Nigeria
Hoto: DW/A. Cascais

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nunar da cewa mutane miliyan 65 da dubu 600 ne ke gudun hijira a sassan duniya daban-daban. Wannan adadi dai ya zarta yawan 'yan gudun hijira na shekara da ta gabata da wanda aka kiyasta yawansu kan abin da bai zarta dubu 300 ba.

Wannan lamarin dai na nuna cewar kowane mutum daya cikin mutane 113 na duniya ya kaurace wa muhallinsa a halin yanzu saboda dalilai daban-daban musamman ma dai yake-yake. Kasashen Syriya da Iraki da Kolombiya na sahun farko na wuraren da aka fi samun 'yan gudun hijira wanda akasarinsu mata ne da yara kanana.

Mata da da kananan yara da dama sun kasance 'yan gudun hijira sakamakon rikice-rikicin da kasashensu ke fuskantaHoto: picture alliance/dpa

Duk da alkawuran da kasashe duniya suka yi a taron da aka gudanar a watan Afirilu a birnin Brussels na kasar Beljiyam, har yanzu hukumar kula da 'yan gudun hijira na ci gaba da mika kokon bararta ga kasashe masu hannu da shuni kan a dafa mata wajen tallafawa wanda wannan matsala ta shafa.

Mafi akasarin 'yan gudun hijira dai sun fito ne daga kasashe 'yan Rabbana ka wadatamu ciki kuwa har da Sudan ta Kudu da Tarayyar Najeriya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wadanda ke fama da rikice-rikice. Galibin mutanen da suka fito daga wadannan kasashe kan ratsa teku don shiga nahiyar Turai da nufin samun ingantaciyyar rayuwa wanda da dama daga cikinsu kan rasa rayukansu yayin wannan yunkuri.