1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar yaki da aiyukan bauta a Nijar

May 4, 2016

A Jamhuriyar Nijar wata kungiya da ke yaki da bauta mai suna TIMIDRIA ta dukufa wajen yaki da wannan dabi'a, inda ta samar da makarantu na koyar da yaran da aka haifa cikin bauta.

Mohamed Mogaze mai fafutukar yaki da bauta a Jamhuriyar Nijar
Mohamed Mogaze mai fafutukar yaki da bauta a Jamhuriyar NijarHoto: DW/J. Henrichmann/F. Quenum

Mohamed Mogaze da shi ma ya fito daga cikin irin wadannan iyalai, ya kudiri aniyar ganinn bayan wannan muguwar dabi'a ta bauta duk kuwa da cewa kokowar tana da wahalar gaske. Gointou Kwara wani karamin gari ne da ke wajen Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar kuma dukkanin mutanen wannan gari an haifesu ne a cikin bauta, sannan akasarin su ba su yi karatun boko ba. Ganin cewa shi ma ya fito ne daga irin wadannan iyalai da aka tilasta musu bauta, Mohamed Mogaze na da masaniyar irin wahalhalun da wannan dabi'a ke jefa mutane. Kungiyarsa ta TIMIDRIA ta lashi takobin ganin bayan wannan dabi'a ta bauta ga baki daya inda suke ilimantar da al'ummar wannan gari na Gointou kwara, ta hanyar koyar da su hakkokinsu a matsayinsu na mutane 'yan Adam sannan kuma ya buda makarantu sabo da koyar da yara kanana, inda ya ce:

"Mu a garemu yara su ne manyan gobe, idan suka yi karatu suka samu ilimi, za su yi kokarin sanin 'yancin su, don haka za su iya tilasta wa iyayensu sanin 'yancin nasu."

A hukumance dai a yanzu za a iya cewa babu wani yaro da ke karkashin bauta a Jamhuriyar ta Nijar, amma kuma a karkashin kasa akwai da dama da ke cikin wannan yanayi. Kuma daya daga cikin dalillan da ya sa ake ganin yara kananan sun fi fuskantar babbar matsala shi ne na karancin samun ilimi. Wannan dalili ne ma ya sanya aka kafa wannan kungiya ta kare hakkin dan Adam da ake kira da TIMIDRIA wadda ke nufin taimakon juna a shekarar 1991. Sannan kungiyar ta watsu a fadin Nijar din baki daya inda a halin yanzu take da cibiyoyin da suke aiki fiye da 180. Ayyukan kungiyar dai na tafiya ne tare da tallafin tsofaffin bayi, inda suke karfafa sanin 'yancinsu tare kuma da koyar da yara kanana.

Yaran da aka haifa cikin bauta sun samu damar zuwa makarantaHoto: DW/J. Henrichmann/F. Quenum

A halin yanzu dai ana iya cewa wannan fafutuka da kungiyar TIMIDRIA ta saka a gaba, na da alamun samun nasara, kasancewar a gari irin su Gointu Kwara yara kanana na cigaba da zuwa makarantu kuma a nan gaba su ne za su zabarma kansu irin rayuwar da suke bukata.