1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da cin hanci na tangal tangal a Najeriya

January 26, 2017

Wasikar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattawan kasar na barazanar tada tsohon liki dama rushe daukacin shirin yaki da hanci a kasar.

Nigeria Symbolbild Muhammadu Buhari Anti-Korruptions-Offensive
Hoto: picture-alliance/AP Photo/C. Owen

Tuni dai masu adawa ta kasar suka hangi kafa sannan kuma suke kokarin kutsawa a cikin yakin hancin tarrayar Najeriyar da ke tangal tangal yanzu.


Wata wasika da shugaban kasar ya aike zuwa majalisar dattawa da kuma a cikinta shugaban yace bashi da niyyar daukar mataki kan sakataren gwamnatin kasar da shugaban hukumar yakar hanci a bisa bayanan da ke gabansa a yanzu. An dai zargi Babachir David lawal da karba na goro daga hannun wani dan kwangilar yankar ciyawa a jihar Yobe. A yayin da kuma majalisar dattawan ta shaidawa Buharin cewar ta samu bayanan sirri daga hukumar tsaron farin kayan DSS cewar shima shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya sha hulda da masu halin bera a kasar.


Wannan dalili ne ya sanya dattawan suka nemi Buhari da ya sauke su daga kujerar su domin kare girma da martabar yaki da cin hanci a kasar.To sai dai kuma a nasa martanin shugaban kasar yace bashi da niyyar yin yadda ake so a bisa bayanan da a cewarsa hujjojin da aka bayar basu gamsar ba. A cikin rikicin ne kuma masu adawar kasar ta Najeriya suka dauka tare da yanke hukuncin cewar gwamnatin kasar ta yi sauyin launi daga yakin da ke kama barayi. Wata sanarwar jamíyyar PDP mai adawa ta ce fadar gwamnatin kasar bata da hurumin sake yakin hancin tun da ta kai ga wanke jamián guda biyu. Abun kuma da a cewar Dr Umar Ardo da ke zaman jigon PDP na kasa ya saba daga matsayin da 'yan kasar ke kallon shugaba Buhari a kansa.

Baki iri biyu a cikin yakar hanci ko kuma kokari na kare barayi a bisa doki na adawa dai, in har masu adawar kasar ta Najeriya su na kallon an kauce a cikin yakin hancin, ga 'ya'yan APC mai mulki, PDP ma bata da abun fada a cikin kasar a halin yanzu, a cewar Isa Tafida Mafindi da ke zaman jigo a cikin jamíyyar APC.

Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba a cikin yakin da a baya ya yi nasarar damke da dama kama daga sojoji ya zuwa alkalai dama su kansu masu takama da siyasar.

Hoto: DW/A. Baba Aminu
Hoto: Reuters/A.Sotunde