Ranar yaki da cin hanci ta duniya
December 9, 2022Yanzu haka dai Matsalar cin hanci da rashawa ta zama ruwan dare gama duniya a tarayyar Najeriya inda kusan ko-wane fanni ana samun matsalar duk da hukumomi na yaki da cin hanci da ake su da kuma matakai na yaki da cin ha ncin da gwamnatin ke ikirarin yi.
Ana ganin wannan matsala ta cin hanci da Rashawa ita ce tushen koma bayan al'amura da ake samu a kasar da su ka hana ta ci gaba.
Gwamnatin Najeriya dai ta samar da hukumomi na tabbatar da yaki da cin hanci amma duk da kokarin da su ke yi ba ga raguwar cin hanci ba wanda ake ganin ana fito da sabbin Salon a wawure kudade daga lalitar gwamnati.
Wannan ma kuma shi ne tuanin Malam Usman Abubakar mai sharhi akn al'amuran yau da kullum a Najeriya.
To sai dai akwai masu ganin matukar ba a dauki tsaurara matakai na hukunta wadan da aka samu da laifin cin hanci da Rashawa baa kwai wuya a iya magance ta tsakanin al'ummar kasar.
Yanzu haka dai da 'yan Najeriya na samun shakku kan shirin yaki da cin hanci na gwamnati inda wasu ke ganin wasu tsiraru ake tuhuma yayin da ake kau da kai daga wasu da ake ganin suna kusa da gwamnati ko kuma shaffafu ne da mai.