Yaki da cin zarafin mata a duniya
November 28, 2019Talla
A yankin arewcain Nigeria ma matan dake zaman aure kan fuskanci muzgunawa daga mazajen su a wasu lokutan ma har da dangin miji. Wani babban nau'in gallazawa da matan ke fuskanta shine yadda wasu mazajen ke aure idan sun ga iyayen matar suna da dukiya idan kuma bayan auren basu sami abin da suke nema ba sai su fara cin zarafin matan. Ana dai yi wa irin wannan aure da lakabi auren jari