1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Yaki da cutar zazzabin cizon sauro

April 25, 2018

Ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bikin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da nufin yin nazari na nasarorin ko akasin haka da aka samu a kokarin magance barnar cutar musamman a kasashen masu tasowa.

Fiebermuecke, Stechmuecke, Anopheles spec., malaria mosquitoe
Hoto: picture alliance/dpa/blickwinkel/Hecker/Sauer

Taken bikin bana wanda ya zo shekaru 70 da hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ke aikin yaki da cutuka shi ne “A shirya a yaki cutar Maleriya”

Ranar bana dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun kwan gaba kwan baya a nasarorin da ake samu wajen yaki da cutar musamman a kasashe ‘yan Rabana ka wadata mu.

Hoto: picture-alliance/dpa7S. Morrison

A shekara ta 2016 rahoton hukumar lafiya ta duniya ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 216 suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro a fadin duniya inda daga ciki mutane dubu 445 suka mutu sanadiyar wannan cuta da aka kashe dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 700 don yaki da cutar a wana shekarar.

Duk da cewa an samu nasarori na rage barnar da cutar ke yi har yanzu cutar na ci gaba da lamushe rayuka al’umma musamman a kasashe irin Najeriya da matakai da ake dauka ba su wadaci yankuna da dama ba.

Ga misali a arewa maso gabashin Najeriya akwai yankuna da dama da tallafin bai isa ba inda wuraren da suka samu kamar sansanonin 'yan gudun hijira ba da yawancin ke zaune a wurare marassa tsabta mutane ba sa iya amfani da gidajen sauro da aka bas u domin kariya daga cutar.

Hoto: picture-alliance/dpa/N. Bothma

Dr Sale Abba wani likita ne da ke aikin agaji a sansanonin 'yan gudun hijira a nan Maiduguri ya ce yawancin wadan da suke zuwa wajen su da maganar rashin lafiya binciken su na nuna musu cewa zazzabin cizon sauro ne.

Gwamnatoci dai na ikirarin sun dauki matakai na yaki da cutar a wadan nan sansanoni da suka hada da fadakarwa da kuma raba gidajen sauro da ma yin feshi sai dai ga alamu matakan ba sa isa wata kila saboda yawan mutanen da ke zaune a sansanoni.

Da yawa daga cikin ‘yan gudun hijirar kuma ba ta gidan sauro su ke yi ba suna fafutkar samun abin sawa a bakn salati ne kamar yadda Muhammad Muhammad wan dan gudun hijira ya shaida min a tattauanawar mu da shi.

Hoto: Eliza Powell

Sai masu yaki da cutar na ganin har yanzu ba a kama hanyar kawar da wannan cut aba ganin an fi bada fifiko wajen bada kariya ko magungunan cutar maimakon yakar shi sauron kan sa da ke yada cutar.

Malam Abu Ubaida Mu’azu masanin kiwon lafiya ne da ke yaki da cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya

Masu yaki da cutar zazzabin cizon sauro sun shawarcin 'yan gudun hijira su ke tsabtace muhallan su tare da tabbatar da amfani da gidajen sauro ga wadan su suka samu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani