Yaki da gurbata muhalli a kasar Cote d'Ivoire
September 2, 2015Yanzu haka dai batun sauyin yanayi na cikin lamarin da ya fi tada hankalin kasashe da-damam, inda masanan ke cewa akasarin abinda ke haddasa sauyin yanayi, dan Adam ne da kansa ke jawo shi, bisa haka ne ma wani matashi a kasar Cote d'Ivoire, ya fara gangamin wayar da kan al'umma bisa gujewa sare datsuka.
Ana wayar da kan al'ummar Cote d' Ivoir bisa samun muhalli mai tsabta. Dan fafutuka Brice Delagneau, shi ne jagoran wannan shirin, inda suka zabi wuri mafi dashewa a ayi gangamin, domin yanki ne da ke haddasa tiririn ababen hawa a birnin Abidjan.
Kurmin Banco yana kusa da Abidjan babban birnin kasar. Ana iya kallonsa daga babban titi. Amma aksarin mazauna birnin ba su taba shiga kurmin ba.
Brice ya karanci ilimin kare mahalli a Abidjan, kuma sai ya kafa tasa kungiyar. Bisa gangamin Brisco na son mazauna Abidjan su fahimci cewa, kurmin Banco shi ne hanyar samar musu da numfashi mai tsabta.
Ba tare da "Kurmin Banco" da mazaunin Abidjan ba zai iya samun iska mai kyau ta ya shaka. Bincike ya nuna cewa, birnin na samun kimanin ton 3000 na gurbatacciyar iska kowace rana. Cike da korayen tsirai, kurmin na baka al'ajabi kamar ba duniya kake ba. Tsakiyarsa an ware shi a matsayin dajin gwamna, da aka mai da shi bangaren shakatawa da ake kula da shi.
Akasarin bishiyoyin da basa cikin inda ake karewan an lalata su. A shekara ta 2009 daukacin wannan kurmin ya kasance ba wurin sa kafa, amma yanzu ya cika da gine-ginen gidaje da masana'antu. Abinda kawai zai iya taimakawa a gyara wajen shi ne shuka sabbin bishiyoyi. Masu halartan shirin suna shuka bishiyoyi daban-daban.
Kudin gudnar da gangamin ana samunsu ne daga taro kare mahalli na shekara-shekara. Sama da bishiyoyi 70 aka shuka yau kadai. Idan masu fafutukar kare muhallin na son ganin amfanin gangamin da suke yi, sukan koma kurmin da ke gefen birnin.
Brice ya yi nasarar jawo hankalin sama da 'yan sa-kai 130 cikin shirin. Ya kuma tsawaita gangamin kare muhallin zuwa makwabtan kasashen Burkina Faso da Ghana.