Yaki da masu kaifin kishin addini a Burtaniya
September 11, 2014Gwamnatin Burtaniya ta bayyana hakan ne bayan da a dan tsakanin nan ake zargin wasu 'yan kasar da kwarara zuwa yankin Gabas ta Tsakiya domin taimakawa kungiyoyi irinsu IS da ke rajin kafa daukar musulunci.
Wannan yanayi da ake ciki ne dai ya sanya mahukuntan na London yanke shawarar daura damarar yaki da masu kaifin kishin addini a kasar, yayin da a hannu guda shugaban darikar Angalikan da ke Burtaniya Archbishop Justin Welby ya ke cewar "wajibi ne mu yi nazari kan musabbabin da ke jawo matasa ke bijirewa, suna daukar tsauraran ra'ayin addini".
To sai dai yayin da shugabannin addinai da sauran jama'a a kasar ke cigaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan yanayi da Burtaniya ke ciki na samun 'yan kasar da shiga kungiyoyin jihadi, a hannun guda da dama na aza ayar tamabayar kan irin tsarin da za ai amfani da shi cike kuma da fatan ganin karshen matsalar.
Duk da dai firaminista Burtaniya David Cameron ya sha alwashin kawar da matsalar a wani jawabi da ya yi gaban majalisar dokokin Britaniya, a hannu guda ya gaza yi wa 'yan majalisar bayani filla-filla kan yadda zai tunkarin matsalar. Wannan dai ya sanya 'yan kasar yin dari-dari da irin yunkurin da mahukuntan kasar suka suna yi kan magance wannan batu.
Mawallafi: Muhammad Sani Dauda
Edita: Ahmed Salisu