1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da wariyar launin fata a Tunusiya

Mahmud Yaya Azare
December 30, 2016

 Lafazin Kahloush, wato "Dan baki", ita ce kalmar da galibin bakaken fata a kasar su ka saba ji ana fada musu a duk sa'ilin da aka so a zolayesu. Abin da 'yan fafutika ke yaki da shi.

Kanada environmental racism - Ingrid Waldron
Hoto: Enrich

Biyo bayan kiraye-kirayen da kungiyoyin kare hakkin bil Adama su kai mata, kan ta dauki matakan kar-ta-kwana, don yaki da nuna wa bakaken 'yan Tunusiya wariyar launun fata da ya yi kamari, gwamnatin kasar taTunusiya ta kaddamar da wani sabon daftarin doka, da zimmar magance matsalar da ke barazana ga zamantakewa a kasar.

Firaministan kasar ta Tunusiya Yusuf Shaheed, wanda ya bukaci mayar da rana ta 26 ga watan Disamba kowace shekara ta zama ranar yaki da nuna wariyar launin fata  ga bakaken kasar, wadanda aka yi kiyasin adadinsu ya kai kashi goma cikin dari na jimullar 'yan kasar.

  "Ya zama wajibi mu dauki irin wadannan matakai a fadin kasa, don yaki da wannan mummunar al'adar da ta yi mana kutse. Matakai ne da ya wajaba mu dasa su tun daga tushe.

Mawaka da 'yan fafutika a Tunusiya na yawan jan kunne kan nuna wariya ga bakar fataHoto: DW

 Lafazin Kahloush, wato "Dan baki", ita ce kalmar da galibin bakaken fata a kasar, su ka saba ji ana fada musu a duk sa'ilin da aka so a zolayesu, ko ai musu izgilanci .Kalmar da wani mawaki bakar fata a kasar Hamza Bin Ashur, ya rera waka ta salon 'yan kama, ya na mayar da martini ga masu aibanta shi don kawai shi baki ne.

Duk da wannan yunkurin da mahukunta ke yi, bakake a kasar na ci gaba da zargin cewa, sun jima su na jin ana gafara sa ba su ga ko kaho ba, lamarin da ya sanya, hattaa ranar da ake gabatar da sabin dokokin yaki da wariyar launin fatar su kai zanga zangar neman ganin sauyi a  kasa, a wannan kasar da ke bugun kirji da zamanta kasa ta farko a Afirka da ta haramta bauta tun shekarar 1890.