Yaki da 'yan bindiga a kasar Masar
May 11, 2015Talla
Kungiyar kabilun da ke yankin Sinai na kasar Masar sun ce za su gama karfi waje guda da nufin yakar kungiyoyin masu kaifin kishin addini ciki kuwa har da 'yan IS da ke tada kayar baya a yankin.
A wani taro da suka ta gudanar 'yan kungiya suka ce sun dau wannan matakin ne don kare gwamnatin kasar da ma dafa mata wajen tabbatar da tsaro a Masar.
Kungiyar da ta kunshi kabilu kimanin talatin wadda ake wa lakabi da Sinai Tribal Federation ta ce za ta yi aiki ne kafada da kafada da hukumomin tsaro na kasar don cimma wannan burin.
Yankin Sinai na kasar ta Masar na daga cikin wurare a kasar da ke fusanta hare-haren 'yan bindiga musamman ma kan jami'an tsaro tun cikin shekara ta 2013.