1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da 'yan bindiga a Najeriya da Nijar

March 25, 2022

Muhawara kan zaman lafiya a kan iyakokin Jamhuriyar Nijar da Najeria a wani mataki na yaki da yan' bindiga da suka addabi kasashen biyu.

Nigeria Niger Friedensgespräche
Hoto: Salissou Kaka/DW

Taron mai taken yaki da ayyukan 'yan ta'adda da 'yan bidiga dadi masu garkuwa da mutane da satar dabbobin al’uma ya hada wakilan bangarorin al'uma da suka hada da sarakunan gargajiya,masu garuruwa da 'yan sanda da shugabannin kananan hukumomi da sauran masu ruwa da taski kan maganar tsaro na Niger da Najeria musammun ma na jihar Maradi da Katsina da Zamfara da kuma Sakoto.

Kwanaki biyu ne dai mahalartan taron za su kwashe suna tafka muhawara kan matsalolin tsaro da suka zamo ruwan dare gama duniya ga kasashen biyu da zumar hada karfi da karfe wurin samun sabbin dubaru na murkushe 'yan bindigar.

Bayanai dai sun nuna cewar bangarorin biyu na zargin juna, bangaren Najeria na zargin galibin makamai na shigowa daga Nijar kasancewar Nijar na tsakanin Najeriya da Libiya inda makaman ke fitowa. Bangaren Nijar kuma na zargin  galibin 'yan bindigar na shigowa ne daga Najeriya.