1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An nada sabbin ministocin Afirka ta Kudu

Zainab Mohammed Abubakar SB
July 5, 2024

Nada sabuwa gwamnatin hadin kan kasa da aka yi a kasar Afirka ta Kudu na ci gaba cikin batutuwa da suka dauki hankalin jaridun Jamus bayan zaben da babu jam'iyyar da ta samu nasara kai tsaye.

Afirka ta Kudu | Cyril Ramaphosa da John Steenhuisen
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu da John Steenhuisen ministan aikin gonaHoto: South African GCIS/AP/picture alliance

Jaridar ta ci gaba da cewa, a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yankin da 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda, ke kutsawa zuwa Han Babban birni na kasuwanci na Butembo, Matasa "yan kishin kasa" da ke yankin ne suka tashi tsaye wajen yakar sojoji da 'yan tawayen da ke addabarsu. A lokacin da 'yan tawayen Kwango na M23 suka mamaye garin Kanyabayonga a karshen makon da ya gabata, kuma suka fara shiga yankunan da yaki bai taba isa ba, firgici ya mamaye babban garin kasuwanci na Butembo mai tazarar kilomita 150 daga arewaci.

Karin Bayani: Afirka a Jaridun Jamus 28.06.2024

Rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar KwangoHoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

Galibin masu zanga-zangar da matasa da aka gaza shawo kan su, sun kafa shingaye a manyan titunan birnin mai na miliyoyi sannan suka fara kai hare-hare kan gidaje, batu da ya tayar da hankalin al'umma da ke rayuwa cikin lumana.

"Jam'iyyu tara da suka wakilci a sabuwar majalisar ministocin Afrika ta Kudu Shugaba Ramaphosa ya gabatar da gwamnatin hadin kan kasa" da haka ne jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta bude sharhin da ta rubuta kan sabuwar gwamnatin gama garin da aka kafa biyo bayan shan kayen da jam'iyyar ANC ta sha a karon farko tarihin kafuwarta.

Sharhin jaridar ya ci gaba da cewar, wata guda bayan zaben 'yan majalisar dokoki a Afirka ta Kudu, shugaba Cyril Ramaphosa ya gabatar da majalisar ministocin "Gwamnatin hadin kan kasa", wadda jam'iyyu tara suka shiga cikinta. Bayan tattaunawa mai zurfi, an cimma matsaya, in ji Ramaphosa a wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar ta talabijin.

John Steenhuisen sabon ministan aikin gona na Afirka ta KuduHoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

A karon farko dai jam'iyyar African National Congress (ANC) ta rasa cikakken rinjayenta tun bayan zaben dimokuradiyya na farko a shekarar 1994, inda aka tilasta mata yin hadin gwiwa da jam'iyyun adawa na baya. Sakamakon ya kasance majalisar zartarwa mai ban sha'awa da ta kunshi ministoci 32 da mataimakansu 43. Jam'iyyar adawa mafi girma, ta Liberal Democratic Alliance (DA), ta samu mukaman ministoci shida, ciki har da ma'aikatar cikin gida mai fama da rikici. Baya ga jam'iyyun ANC, da DA da kuma jam'iyyar Zulu Inkatha Freedom Party (IFP), wadda ke da muhimmanci a lardin KwaZulu-Natal, akwai wasu kananan jam'iyyu shida cikin gwamnati hadin kan kasar ta Afirka ta Kudu.

Ita kuwa jaridar Zeit Online nazari ta yi kan rikicin zanga zangar matasa da Kenya, inda a wannan makon ne aka yi sake yin wata zanga zangar nuna adaw dawa da gwamnatin kasar tare da tunawa da 'yan uwansu 39 da suka rasa rayukansu lokacin rikicin haraji.

Amfani da karfi kan masu zanga-zanga a KenyaHoto: Shisia Wasilwa/DW

Duk da janye dokar haraji mai cike da cece-kuce, ana ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba William Ruto a Kenya in ji jaridar. 'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan wasu kananan gungun masu zanga-zanga a birnin Nairobi. Dakarun 'yan sanda kuma sun rufe hanyoyin shiga majalisar da fadar shugaban kasa. Shagunan da yawa a tsakiyar birnin sun kasance a rufe.

A tsakiyar birnin Mombasa, birni na biyu mafi girma a kasar, daruruwan mutane sun sake taruwa dauke da vuvuzela, da tutocin Kenya da alamun "Dole ne Ruto ya tafi". A Kisumu da ke yammacin Kenya, masu zanga-zangar sun kuma yi ta rera waka na neman shugaban ya yi murabus duk da yawan jami'an 'yan sanda. Suna zarginsa da tsadar rayuwa a kasar da ke gabashin Afirka, wanda da kyar mutane da yawa za su iya biya. An kashe mutane 39, sama da 360 suka jikkata, a cewar hukumar kare hakkin dan Adam ta Kenya, lokacin da ‘yan sanda suka harba harsashi mai rai kan masu zanga-zangar.