Siriya: MDD ta koka kan halin da ake ciki a Idlib
February 19, 2020Majalisar Dinkin Duniya ta yi kashedin cewa, akalla mutane dubu 900 sun rasa muhallansu sakamakon hare-haren dakarun kawancen Siriya da Rasha kan ragowar mayakan ‘yan tawaye a lardin Idlib da ke Arewa maso yammacin kasar, tun daga watan Disamba na bara kawo yanzu. Tayseer Goodah,shi ne wakilin kungiyar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Idlib,ya kumna yi karin bayani kan irin mawuyacin halin da 'yan gudun hijirar ke ciki, a iyakar Siriya daTurkiya:
"Akwai 'yan gudun hijira fiye da dubu 900 a yankin Idlib. Tsofi da Jarirai da kananan yara na ci gaba da mutuwa saboda matsalar cinkoso a sansanonin ‘yan gudun hijira a dai dai lokacin da ake tsananin sanyi a arewacin kasar ta Syria,wanda ya kai awo biya ƙasa da sufili a ma'aunin Celsius."
Wani magidanci daga cikin wadanda suka samu tsallakewa da baya suka baro yankin Marrah Nu,man da dakarun Siriya da jiragen yakin Rasha suka yi wa raga-raga, ya bayyana takaicinsa ga yadda duniya ta juya musu baya ana ta yi musu kisan kiyashi:
"Ina za mu sa kanmu a wannan duniyar? Muna zaune lafiya cikin gidajenmu, sukai ta yi mana lugudan rokoki ta sama da kasa cikin dare. Gashi yanzu munzo nan a watsarmu a filin Allah. Ba abinci ba ruwa ba barguna. Ina mutanan duniya suke ne? Ina 'yan uwanmu Larabawa suke? Allah ya isanmu."
Shugaban hukumar agajin Majalisar Dinkin Duniya Mark Lowcock, ya ce rikicin yankin Arewa maso yammacin kasar ta Syria ya yi matukar muni, kuma fafaren hula ne suka fi dandana kudarsu a cikinsa:
"Rahotonni da muke samu daga wakilan agaji a 'yan kwanakin baya-bayan nan, na nuni da samuwar mace-macen farararen hula sakamakon raunukan da suka samu da kuma rashin magunguna.Yara kanana na sandarewa saboda tsananin sanyi. Iyaye na daukar matakin kona robobi dan taimaka wa ‘ya’yansu domin jin dumi. Sai dai kananan yara da ma jarirai na ci gaba da mutuwa sakamakon tsananin da suke fuskanta. Halin da suke ciki abun takaici da kunya ne ga kasashen duniya. Muna kira da bangarorin da ke gwabzawa da juna su kwan da sanin cewa, hakkin fafaren hular da ba su san hawa ba su san sauka ba, ba zai tafi a banza ba. Dole ne su mutunta hakkokin masu bukatar agaji a ko'ina suke ,a kuma kowane lokaci."
Tun a Afrilun shekarar 2019 ne dai, dakarun gwamnatin Asad, wadanda jiragen yakin Rasha ke wa sharar fage, suka kaddamar da hare-haren da Shugaba Asad ya siffanta na a yita ta kare ne, kan yankin na Idlib ,da ke zama tungar karshe ta 'yan tawaye, duk kuwa da yarjejeniyar dakatar da buda wutar da aka cimma a birnin Sochi, a watan Satumbar shekarar 2018, yarjejeniyar da ta dora wa Rasha da Turkiya alhakin shiga tsakani don ganin an aiwatar da ita sau da kafa.