Yaki ya ki ci ya ki cinyewa a Afirka ta Tsakiya
February 13, 2014Talla
Kisan kai da kwasar ganima, su ne manyan matsalolin da 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ke fuskanta kama daga babban birnin ƙasar wato Bangui zuwa sassa daban daban na ƙasar. Duk kuwa da sojojin ƙasashen wajen dake ƙasar bai hana al'ummarta shiga cikin halin ha-ula'i ba inda ko a cikin farkon watan Fabrairun nan al'ummar dake zaune a ƙauyen Nzakun dake da iyaka da ƙasar Cadi ta fuskanci muguwar ta'asa ta kisan gilla.