Yaki ya sa bazuwar makamai a Gabas ta tsakiya
March 12, 2018Talla
Adadin makamai da kasashen duniya ke shigo da su yankin Gabas ta tsakiya ya karu da kashi 103 a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2017. Rahoton na SIPRI ya nuna kasar Saudiyya na kan gaba wajen shigo da makamai a kasar Yemen, sakamakon yaki da take yi da 'yan tawayen Houthi.
Amirka ta kasance kasar da tafi kowace yawan fitar da makamai a shekaru biyar da suka gabata, inda aka zargeta da sayar da mafi yawan makamai da ake yaki da su a kasahen Gabas ta tsakiya.