Yakin Aleppo ya killace kimanin mutane miliyan daya
November 22, 2016![Syrien Aleppo Bergung aus zerstörtem Gebäude](https://static.dw.com/image/36455129_800.webp)
Talla
Sai dai babban jami‘in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Stephen O‘Brien, ya shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar a wannan Litinin cewa a yanzu adadin mutanen da yakin ya ritsa da su a birnin na Aleppo da kewayensa ya tashi daga kusan mutun dubu 400 a baya zuwa miliyan daya a halin yanzu.
Kuma ya zargi mahukuntan Siriyar da daukar matakin barin mutanen a cikin yunwa da haramta kai masu duk wani dauki ko agaji domin tilasta masu tserewa daga gidajensu.