Kwanaki 100 na luguden wuta da farautar 'yan Hamas a Gaza
January 14, 2024Isra'ila ta ce ba wani abinda zai hanata ci gaba da kare manufofinta na kakkabe mayakan kungiyar Hamas daga Zirin Gaza, a yayin da yakin da ake gwabzawa tsakanin kasar da Hamas ya cika kwanaki 100.
A cikin wani taron manema labarai a birnin Tel-Aviv, Firaminista Benjamin Netanyahu, ya ce ba wanda zai iya dakatar da manufofin da Isra'ila ta sa gaba na kawar da barazanar da take fuskanta daga Zirin Gaza.
Karin Bayani : Antony Blinken ya yi tozali da Mahmud Abbas kan rikicin Hamas da Isra'ila
Wasu iyalan Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su, sun yi zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan garkuwa da danginsu da ake ci gaba da yi, a yayin da wasu dumbin magoya bayan a dakatar da yakin da Isra'ila ke yi da Hamas, suka yi zanga-zangar neman a tsagaita buda wuta don shigar da kayayakin agaji a Gaza.
Karin Bayani : Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun kasa da kasa
Luguden wutar da Isra'ila a sassan Gaza, a kokarinta na kakkabe mayakan Hamas da wasu manyan kasashe suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda, ya kashe Falasdinawa fiye da dubu 23 a cewar ma'aikatar lafiyar yankin Falasdinu.