SiyasaGabas ta Tsakiya
Yakin Iran na fadada
March 30, 2026
Talla
Shugaban majalisar gudawawar Tarayyar Turai, Antonio Costa ya yaba da tattaunawa ta wayar tarho tare da Firaminista Shehbaz Sharif na kasar Pakistan, kan batun samar da mafita na kawo karshen yaki a Iran, bayan kasashen Amurka da Isra'ila sun kaddamar da farmaki kan kasar.
Tattaunawa
Ita dai Pakistan ta karbi taron ministocin harkokin wajen kasashen Masar da Saudiyya, da Turkiyya a birnin Islamabad na kasar ta Pakistan.
Wannan na zuwa lokacin da Iran take cewa wuraren tarhi na kasar kimanin 130 aka lalata sakamakon hare-haren kasashen Amurka da Isra'ila. A birnin Tehran fadar gwamnatin Iran kadai kimanin wuraren tarihi 61 aka lalata a cewar gwamnatin kasar.