1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin kasar Siriya ya mamaye taron G8

Usman ShehuJune 18, 2013

An kammala taron kungiyar kasashe takwas da suka karfin masana'antu a duniya wato G8, inda yakin kasar Siriya kankane taron

U.S. President Barack Obama (L) meets with Russian President Vladimir Putin during the G8 Summit at Lough Erne in Enniskillen, Northern Ireland June 17, 2013. REUTERS/Kevin Lamarque (NORTHERN IRELAND - Tags: POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY)--eingestellt von haz
Shugaban Amirka Obama da na Rasha PutinHoto: Reuters

Shugaban kasar Amirka Barack Obama yana ziyara a kasar Jamus, Shugaba Obama, a yau Talata ya iso Berlin inda zai gana da mahukuntan Jamus gabanin tattaunawar da za a yi gobe Laraba, tsakanin kungiyar Tarayyar Turai da Amirka, wanda za ta mai da hankali kan harkar kasuwanci. Kafin ya isa kasar Jamus shugaban kasar ta Amirka ya halarci taron kungiyar G8, indarikicin Siriya ya mamaye taron.Tattaunawa kan rikicin kasar Siriya da aka yi tsakanin shugaban kasar ta Amirka Barack Obama da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ya kare banza. Shugabannin sun tattauna gaba da gaba a gefen taron G8, wanda rarrabuwar kawuna kan rikicin Siriya ya mamaye jadawalin taron baki daya. Gabanin ganawar ta su dai, Putin ya soki shelar da Amirka ta yi na baiwa 'yan tawayen Siriya mamakai, inda Rasha ta ce hujjar cewa Assad ya yi amfani da makamai mai guba bashi da inganci. Bayan ganawarsu, Putin ya fadawa manema labarai cewa "Matsayinmu bai zo daya ba, amma dukkan mu biyu, mun yarda cewa dole akawo karshen tashin hankalin, domin rage zubar da jini da ake yi a Siriya. Kana a warware tashin hankalin bisa tattaunawa"

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu