1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yarfen siyasa a yakin neman zabe

Uwais Abubakar Idris YB
January 2, 2019

A Najeriya yakin neman zaben kasar da za a yi a wata mai zuwa na kara zafi inda manyan jam'iyyun siyasu biyu ke yarfar juna maimakon kamfe bisa akida ta siyasa da ma batutuwan da suka shafi jama’a.

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Hoto: Atiku Media Office

Lamarin dai ya sanya nuna damuwa a kan illar da wannan salo na yarfen siyasa ka iya yi a dimukuradiyyar kasar, a daidai lokacin da ake neman gudanar da zabe bisa lumana da kwanciyar hankali a shekaran nan.

Tun daga lokacin da aka yaye kallabi na yakin neman zaben a Najeriya aka yi fatan cewa a bana za a samu sauyi  daga ‘yan siyasa saboda manyan ‘yan takara biyu na jamiyyar APC mai mulki da PDP ta ‘yan adawa dukkaninsu daga bangare daya suka fito na kasar. To sai dai ta bayyana cewa sun gaza inda suke furta kalamai na yarfe irin na siyasar da ya kamata a ce an wuce wannan matsayi a siyasar Najeriyar, wacce shekaru ashirin cur da sake girka ta ko ba komai ya kamata a ce sun koyi darasi. Dakta Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da ke jami’ar Abuja ya ce rashin abin fada ne ya sanya wannan hallaya.

Magoya baya sun wasa wuka ana yarfar junaHoto: DW

Duka bangarorin biyu dai sun buge ne a kan batu na cin hanci da rashawa da suke nuna wa juna yatsa har ma da kama suna na cewa barawo ne ke ihun a kama barawo, maimakon yi wa ‘yan Najeriya bayanin irin manufofin da suke da su ko kuwa alkawarin shawo kan matsalolin da suke zayyane a fili. Kama daga rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki da rashn aikin yi ga koma bayan ilimi.

Tuni dai matasan ‘yan siyasa irin su Sulaiman Ibrahim Gaga ke bayyana rashin gamsuwa da wannan salon a kamfe da suke ganin ba zai kai kasar ko’ina ba. A bisa tsari dai hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriyar ce ya kamata a ce tana tsawatarwa a kan lamarin amma kuma shiru ka ke ji, abin da ke sanya yi mata kallon gazawa.

Kwararru na bayyana cewa akwai bukatar ‘yan siyasar Najeriya su sanya wa bakinsu linzami a yakin neman zaben da suke yi domin samun gudanar da babban zaben na Najeriya cikin kwanciyar hankali don dorewar tsarin na dimukuradiyya da shi ne sandar duka garesu baki daya.