1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha: Ukraine ta zafafa hare-hare a Kursk

August 21, 2024

Dakarun Ukraine na ci gaba da kutsa kai cikin Kursk na Rasha, inda suka yi ikrarin lalata gadoji a yankin da ke ta matukar tasiri ga Moscow a yakin da take yi da Kyiv din.

Ukraine | Hare-Hare |  Rasha | Kursk
Ukraine na zafafa hare-harenta a yankin Kursk na RashaHoto: 95th Air Assault Brigade/via REUTERS

A yanzu haka dai Ukraine ta yi ikrarin kwace kimanin kaso uku na Kursk da ke Rashan, lamarin da ya sanya Moscow ta kwashe fiye da mutane dubu 120 daga yankin mai yawan al'umma kimanin miliyan daya. Dalilan da suka sa wannan yankin ke da matukar muhimmanci ga Rasha su ne, yana dauke da tashar jirgin saman sojojinta a wajen inda Kyiv ta kwace iko da shi kuma Rashar na amfani da wannan tashar wajen kai hare-hare cikin Ukraine. Kazalika Rasha na amfani da yankin Kursk, wajen aike dakaru da kuma kayan aiki zuwa Ukraine.

Karin Bayani: Shekaru 25 Putin na harkar mulki a Rasha

A yanzu dai zai yi matukar wuya ga Moscow ta iya isa ga dakarunta a lokacin da take bukata, sakamakon lalata wasu gadoji da Ukraine ta yi a karshen makon da ya gabata da kuma farkon wannan mako. Hukumomin Rasha sun ce Ukraine ta lalata kimanin gadoji uku da ke kan Kogin Seym, tun bayan da Kyiv din ta fara zafafa kai farmaki yammacin kasar a farkon watan Augustan da muke ciki. Ko da yake Rasha ta ce tana sake sabon shiri, sai dai kuma a cewar Maria Zakharova kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rashan yunkurin Ukraine na tunkarar yankin zai mayar da hannun agogo baya a tattaunawar zaman lafiya domin shawo kan rikicin.

Rasha ta ce tana kokarin dakile hare-haren Ukraine a yankin KurskHoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Tun da fari Ukraine ta yi ikrarin cewa zafafa kai farmaki yankin na Kursk ba wani yunkuri ba ne da kwace iko da Rasha ko kuma ta mamaye ta ba, sai dai tana daukar matakan kariya ne da ma shata iyaka da nufin rage karfin tasirin hare-hare da Moscow ke kai mata daga yankin. Ana dai ganin Ukraine tana amfani da wasu makamai ne da Amurka ta  aike mata wajen kai wadannan hare-hare, sai dai har yanzu gwamnatin Washingnton ba ta ce uffan ba kan wannan zargin na Kyiv na amfani da makaman Amirka, sai dai Amirka ta jadadda cewa har yanzu bata sauya manufofinta.

Karin Bayani: Nahiyar Turai na cikin halin tsaka mai wuya

Sai dai kuma a cewarta, Kyiv na kare kanta ne daga hare-haren Rasha, kamar yadda wani kwamandan rundunar M777 ta Ukraine ya gargadi Rasha kan cewa hawainiyarta ta kiyayi ramarsu. Idan har Ukraine na so ta yiwa Rasha iyaka a wannan yakin da suke gwabzawa, tana bukatar ci gaba da kwace iko da yankin. Ko da yake, tuni ta fara dasa nakiyoyi domin kare wuraren da ta kwace iko da sun. Yayin da Kyiv din ke kara fadada iyakar da za ta shata da Rasha, hakan zai kara bai Moscow wahala wajen kai hari cikin makwabciyar tata.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani