1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yakin Sudan: al-Burhan ya yi garambawul a ministocinsa

November 4, 2024

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya yi garambawul ga majalisar ministocinsa inda ya sallami ministan harkokin waje da kuma ministan yada labarai har ma da wasu hafsoshin sojin kasar.

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan a yayin da yake  jawabi a birnin Khartoum, 2022
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan a yayin da yake jawabi a birnin Khartoum, 2022Hoto: ASHRAF SHAZLY/AFP/Getty Images

Shugaban ya sanar da hakan ne a daidai lokacin da kasar ke tsaka da yaki har ma da tsananin bukatar kayan agajin jinkai da kuma tunkarar kalubalen 'yan gudun hijra a kasar da yaki ya daidaita.

Karin bayani: Harin RSF a yankin Darfur na Sudan ya halaka mutane 12

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ke kiraye-kirayen tsagaita bude wuta da kuma dakatar da yakin da ake gwabzawa a yankin al-Jazira, da ke kudancin babban birnin Khartoum, wanda hakan ke shafar dubban mutanen da ke yankin.