1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yakin Sudan: Kungiyar IGAD ta bukaci maslaha ta dindindin

December 30, 2024

Jakadan kungiyar bunkasa ci gaban kasashen gabashin Afrika IGAD a Sudan ya ce shirye-shirye sun kammala na zuwa kasar domin warware takaddamar da ke tsakanin bangarorin da ke gwabza yaki a kasar.

Janar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo
Janar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo Hoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

A baya dai kungiyar ta IGAD tare da hadin gwiwa da kasashen Amurka da Saudiyya sun shiga tsakani, duk da cewa an kasa cimma matsaya wajen warware takaddamar da ke tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan da ke jagorantar gwamnatin rikon kwaryar kasar da kuma shugaban rundunar kar-ta-kwana ta RSF Mohamed Hamdan Daglo.

Karin bayani: Sudan ta katse hulda da kungiyar IGAD

A watan Janairun 2024, kungiyar ta bunkasa ci gaban kasashen gabashin Afrika ta gayyaci Hamdan Daglo taronta a Uganda, matakin da ya harzuka gwamnatin Sudan inda ta zargi IGAD da son zuciya.

Karin bayani: Taron shugabannin kasashen Kungiyar IGAD

Jakadan na IGAD Lawrence Korbandy, ya ce yana fatan a samar da masalaha ta dindindin wajen kawo karshen yakin Sudan a ziyarar da zai kai yankin Port Sudan a watan Janairu.